Atiku: Banyi Watsi Da Wike Ba, Na zabi Dan Takarar Da Zan Iya Aiki Da Shi ne

Atiku: Banyi Watsi Da Wike Ba, Na zabi Dan Takarar Da Zan Iya Aiki Da Shi ne

  • Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ce bai zabi Wike a matsayin abokin takararsa ba, saboda yana son wanda zai yi aiki da shi cikin aminci
  • Atiku Abubakar ya dauki Ifeanyi Okowa a matsayin abokin takararsa a zaben shugaban kasa na 2023
  • Alhaji Atiku Abubakar ya ce yayi imani gwamnan Jihar Rivers Nyesome Wike zai yi fice a siyasar Najeriya nan gaba

Abuja - Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ce bai zabi Nyesom Wike, gwamnan Rivers, a matsayin abokin takararsa ba, saboda yana son wanda zai yi aiki da shi cikin aminci.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da yayi da Arise TV ranar Juma'a.

Dan takarar na PDP ya zabi Ifeanyi Okowa, gwamnan Delta, a matsayin abokin takararsa a zaben shugaban kasa na 2023, duk da cewa kwamitin gudanarwa na jam’iyyar (NWC) ta amince da Wike a matsayin mataimakinsa.

Kara karanta wannan

2023: Sabon sabani ya kunno kai a APC kan wanda Tinubu ya zaba mataimaki, Gwamna El-Rufa'i ya fusata

ATIKU
Atiku: Ban kin Daukar Wike nayi Ba Na zabi Dan Takarar Da Zan Iya Aiki Da Shine Cikin Aminci FOTO Legit.NG
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Zabin dai ya janyo matsala a cikin jam'iyyar, inda wasu gungun masu ruwa da tsaki suka dage cewa a dauki Wike.

Da yake magana akan zabin dan takarar mataimakin shugaban kasa, Atiku yace ya zabi Okowa ne maimakon Wike saboda yana son wanda zai iya sadar da manufofin jam’iyyar.

Atiku ya ce:

“Ba kin amincewa da Gwamna Wike aka yi ba. Babu wanda ake ki a jam’iyyar. Amma dole ne ku fahimci cewa hakkin dan takara ne ya zabi abokin takararsa wanda ya yi imanin zai iya yin aiki da shi cikin lumana,
"Sannan kuma ya sadar da manufofin jam'iyyar, da kokarin wajen hada kan al'ummar kasar.
“Gwamna Wike hazikin dan siyasa ne mara tsoro na yi imani zai yi fice a siyasar Najeriya nan gaba.

Kara karanta wannan

2023: Ba don ra'ayin kaina na zabi Shettima ba, Tinubu ya fadi dalilin zabo mataimakinsa

Gwamnonin APC sun so Zulum ya zama abokin takarar Tinubu, Shettima ya fadawa Buhari

A wani labari kuma, Abuja - Kashim Shettima ya fadawa shugaba Buhari cewa Gwamnonin APC sun so Zulum ya zama abokin takarar Tinubu kamar yadda PREMIUM TIMES ta rawaito.

Shettima ya nemi shugaba Buhari ya yiwa Zulum godiya akan yadda ya rika ambaton sunan sa, a duk lokacin da aka masa tayin zama abokin takarar Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Tofa avatar

Ibrahim Tofa