Atiku yana ganin Buhari ya yi abin da ya cancanci yabo, ya jinjinawa Shugaban kasa

Atiku yana ganin Buhari ya yi abin da ya cancanci yabo, ya jinjinawa Shugaban kasa

  • Alhaji Atiku Abubakar ya yi magana da gwamnatin tarayya ta maida NNPC kamfanin kasuwanci
  • ‘Dan takaran na jam’iyyar PDP yana ganin gwamnatin Muhammadu Buhari ta kama hanyar gyara
  • Har yanzu Atiku bai cire rai NNPP zai koma hannun ‘yan kasuwa kamar yadda aka yi a su Saudi ba

FCT, Abuja - ‘Dan takara a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya yabi gwamnatin tarayya saboda matakin da ta dauka na maida NNPC kamfanin kasuwanci.

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana haka ne da yake bayani a shafinsa na Twitter a ranar Laraba, 20 ga watan Yuli 2022.

‘Dan takaran ya ce wannan mataki da aka dauka yana cikin manufofinsa domin ganin an yi garambawul ta yadda gwamnati za ta rika cin riba sosai.

Punch ta rahoto Atiku yana cewa yin hakan zai taimaka wajen ganin an gyara bangaren mai da gas.

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar na cikin koshin lafiya, in ji Mai magana da yawunsa

Ina fatan karasa aikin - Atiku

A jawabin da ya yi a shafinsa, ‘dan takaran shugaban kasar yake cewa yana fatan zai karasa abin da yake da shi a rai, na mallakawa ‘yan kasuwa NNPC.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Burin Atiku Abubakar shi ne NNPC ya zama tamkar kamfanin NLNG da ‘yan kasuwa ke da jari.

Atiku Abubakar
'Dan takaran Shugaban kasa, Atiku Abubakar Hoto: @Atiku.org
Asali: Facebook

Wazirin na Adamawa ya kuma bada misali da Saudi da ta saida kamfanin man ta na Aramco da kuma Petrobras da kasar Brazil ta ba mutane damar zuba kudinsu.

Abin da Atiku ya fada

“A shekarar 2018, na fadawa Duniya niyyar da nake da ita na gyara NNPC domin ganin ta rika cin riba sosai, a tabbatar da gaskiya keke-da-keke, kuma ya rika aiki da kyau.”
“Gwamnatin da APC ta ke jagoranta, ta yi mani kaca-kaca saboda hangen nesa na kishin-kasa. Amma yau ina murya, gwamnatin nan ta kama hanyar layin shawarar da na bada.”

Kara karanta wannan

Saura kiris: Muna ta kokarin kawo karshen yajin aikin ASUU, inji gwamnatin Buhari

“Wannan mataki da aka dauka ya yi kyau, amma har yanzu akwai sauran aiki a kan abin da nake so.
“Ina fatan zan samu damar maida NNPP tamkar NLNG, da Aramco na kasar Saudi Arabia da Petrobras na Brazil, yadda mutane da kamfanonin Najeriya za su sa kudinsu a ciki.”

Ganduje da bashin N10bn

Kungiyar Kano First Forum ta na kalubalantar Gwamnati, ta nemi a hana Abdullahi Umar Ganduje cin bashin Biliyoyin kudi da nufin kafa na'urorin CCTV.

A jiya aka samu rahoto Lauyoyin Mai girma Abdullahi Umar Ganduje sun yi galaba a kan Lauyoyin KFF, Alkali ya ce za a iya karbo bashin kudin da ake so.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng