Yanzu-yanzu : Buhari ya gana da Shettima bayan an kaddamar da shi abokin takarar Tinubu
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da Kashim Shettima bayan an kaddamar da shi mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar APC
- Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum yana cikin tawagar da suka raka Kashim Shettima fadar shugaban kasa
- Kaddamar da Kashim Shettima a matsayin abokin takarar Tinubu ya janyo suka daga kungiyoyin daban-daban a fadin kasar
Abuja - Dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar APC, Kashim Shettima, ya kai wa shugaba Buhari ziyara a fadar gwamnati da ke Abuja bayan an kaddamar dashi abokin takarar Tinubu. Rahoton PUNCH
Gwamnan jihar Borno yana cikin tawagar da suka raka Kashim Shettima fadar shugaban kasar da misalin karfe 04:00 na yammacin ranar Laraba.
Ganawar na zuwa ne sa’o’i bayan an kaddamar da Shettima a matsayin abokin takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu kamar yadda jaridar THE NATION ta rawaito.
Da ya ziyarci shugaban kasa a gidansa da ke Daura a ranar 10 ga watan Yuli, Tinubu ya bayyana cewa ya zabi Shettima ne saboda hazakar shi da kuma mutum ne da zai iya dogaro da shi.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Daukar Shettima a matsayin abokin takarar Tinubu kuma kasancewar su duka Musulmai ya janyo kakkausar suka daga kungiyoyi daban-daban a fadin kasar.
Buhari ya umarci ministoci da su bayyana nasarorin gwamnatin sa cikin shekaru 7
A wani labari kuma, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umurci ministoci da shugabannin ma’aikatu da hukumomi da su bayyana nasarorin da gwamnatinsa ta samu cikin shekaru bakwai da suka gabata. Rahoton THISDAY
Ya kuma bayyana cewa a karkashin kulawar sa an kammala ayyukan muhalli sama da 266 a fadin kasar tun daga shekarar 2015.
Asali: Legit.ng