Da Dumi-Ɗumi: Sabuwar matsala, Ɗan takarar gwamna kuma babban Jigo ya fice daga APC

Da Dumi-Ɗumi: Sabuwar matsala, Ɗan takarar gwamna kuma babban Jigo ya fice daga APC

  • Tsohon Sanata mai wakiltar kudu maso gabashin jihar Ribas, Sanata Magnus Abe, ya fice daga jam'iyyar APC
  • Abe, wanda ya nemi tikitin takarar gwamnan jihar, ya ce ya jima da barin APC, amma yana nan tare da Bola Tinubu a 2023
  • Har yanzu dai APC reshen jihar na fama da guguwar sauya sheka tun bayan kammala zaɓen fidda gwani

Rivers - Tsohon Sanata mai wakiltar mazaɓar jihar Ribas ta kudu maso gabas a majalisar Dattawa, Sanata Magnus Abe, ya fice daga jam'iyyar APC, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Sanata Abe, a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Parry Benson, ya fitar ranar Laraba da tsakar rana, ya sha alwashin cigaba da goyon bayan ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Hotuna sun bayyana, Tinubu ya kaddamar da Shettima a Abuja

Magnus Abe.
Da Dumi-Ɗumi: Sabuwar matsala, Ɗan takarar gwamna kuma babban Jigo ya fice daga APC Hoto: Magnus Abe/facebook
Asali: Facebook

A sanarwan, Sanata Abe ya ce:

"Na daɗe da barin jam'iyyar APC reshen jihar Ribas, amma har yau ina tare da gidan Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, kuma bani da wata matsala da shi ko kaɗan."

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Abubuwa sun dagule wa APC a Ribas

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa Sanata Abe na takun saƙa da wasu manyan jiga-jigan jam'iyyar APC a jihar Ribas.

A wani rahoton baya-bayan nan da Channels tv ta tattara, kafin ficewarsa daga APC, Sanata Abe ya bayyana cewa ba zai mara baya ga ɗan takarar gwamnan Ribas da jam'iyya ta tsayar ba a zaɓen 2023.

Abe, wanda ya nemi ya gaji kujerar gwamna Wike na PDP a zaɓe na gaba, ya ce ba zai marawa ɗan takarar baya ba saboda a tunaninsa bai taka matakin ba a siyasance.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Masu Gidajen Burodi Za Su Tsinduma Yajin Aiki Na Kasa Baki Daya A Najeriya

Ya bayyana Mista Cole (Ɗan takarar gwamnan APC) da mutum wanda bai taba baiwa jihar Ribas wata gudummuwa ba a kowace kujerar siyasa.

Bugu da ƙari, tsohon sanatan ya ce ɗan takarar da APC ta tsayar yanzu haka yana fama da zarge-zargen cin hanci da rashawa.

A wani labarin kuma mun haɗa muku Jerin gwamnonin da suka sha ƙasa a zaɓe yayin da suka yi yunƙurin tazarce kan kujerun su a Najeriya

A wasu lokutan Gwamnonin da ke kan madafun iko kan rasa damar tazarce a Najeriya, a baya-bayan nan mutane sun shaida yadda karfin mulki ya gaza a zaɓen Osun da aka kammala.

Wasu gwamnoni a Najeriya sun sha kaye yayin da suka yi yunkurin ganin sun zarce zango na biyu a kan kujerun su a lokuta daban-daban.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262