Buhari ya umarci ministoci da su bayyana nasarorin gwamnatin sa cikin shekaru 7

Buhari ya umarci ministoci da su bayyana nasarorin gwamnatin sa cikin shekaru 7

  • Shugaba Buhari ya umurci ministoci da shugabannin ma’aikatu da su bayyana nasarorin da gwamnatinsa ta samu cikin shekaru bakwai da suka gabata
  • Buhari ya yaba wa Sakataren Gwamnatin Tarayya da Kwamitin Gudanarwa na Ofishin Kula da Muhalli (EPO), kan gudanar da ayyuka yadda ya kamata
  • Shugaba Buhari ya ce karkashin kulawar sa an kammala ayyukan muhalli sama da 266 a fadin kasar

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umurci ministoci da shugabannin ma’aikatu da hukumomi da su bayyana nasarorin da gwamnatinsa ta samu cikin shekaru bakwai da suka gabata. Rahoton THISDAY

Ya kuma bayyana cewa a karkashin kulawar sa an kammala ayyukan muhalli sama da 266 a fadin kasar tun daga shekarar 2015.

Da yake magana a ranar Laraba a fadar gwamnati da ke Abuja, yayin da yake kaddamar da wani taro na ayyukan muhalli da gwamnatinsa ta gudanar.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Buhari ya fusata, ya fadi ranar da yake so ASUU su janye yajin aiki

Buhari
Buhari ya umarci ministoci da shugabannin ma'aikatu da su bayyana nasarorin gwamnatin sa cikin shekaru bakwai FOTO Legit.NG
Asali: Twitter

Shugaban ya umurci ma’aikatu da hukumomin ba tare da bata lokaci ba su nuna ayyukansu da nasarorin da suka samu ga jama’a.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya bayyana cewa an kaddamar ayyukan muhalli guda 332, daga cikinsu an kammala 266 yayin da sauran 66 suna mataki daban-daban na kammalawa.

Shugaban wanda ya kaddamar da littafin kafin a fara taron mako-mako na Majalisar Zartaswa ta Tarayya (FEC), inda ya yaba wa Sakataren Gwamnatin Tarayya da Kwamitin Gudanarwa na Ofishin Kula da Muhalli (EPO), bisa yadda suka yi amfani da damar su wajen aiwatar da ingantaccen ayyukan da aka amince da su.

Gudaji Kazaure: Na sauya sheka daga APC zuwa ADC, amma har gobe ni dan kashenin Buhari ne

A wani labari kuma, Dan majalisar wakilai ta kasa daga jihar Jigawa, Muhammad Gudaji Kazaure, ya bayyana cewa ya sauya sheka daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) zuwa African Democratic Congress (ADC).

Kara karanta wannan

Buhari ya nema a kafa kotun yaki da cin hanci da rashawa a nahiyan Afrika

Sai dai kuma, Kazaure ya ce har yanzu yana nan a matsayinsa na dan kashenin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne, jaridar The Cable ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Tofa avatar

Ibrahim Tofa