Gwamna Oyetola zai kalubalanci sakamakon zaben Osun da lauyoyi 50
- Gwamnan jihar Osun, Gboyega Oyetola na jam’iyyar APC ya shirya kalubalantar zaben Osun da lauyoyi 50
- Sanata Ademola Adeleke ya doke Gboyega Oyetola zaben gwamnan Osun da aka gudanar a ranar Asabar
- Jam'iyyar PDP ta ce kalubalantar nasarar zaben Senata Adeleke a kotu, kamar yiwa Lauyoyi kyautar kudi
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Jihar Osun - Gwamnan jihar Osun, Gboyega Oyetola kuma dan takarar jam’iyyar APC a zaben gwamna da aka kammala a jihar ya shirya tsaf domin kalubalantar zaben a kotu. Rahoton VANGUARD
Dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP, Sanata Ademola Adeleke ya lashe zaben gwamnan Osun da aka gudanar a ranar Asabar, 16 ga Yuli, 2022.
Adeleke ya samu kuri’u 403,371 a PDP inda ya doke Oyetola da APC da kuri’u 375,027, inda Lasun Yusuf na Labour Party, LP ya samu kuri’u 2,729.
Da yake magana da VANGUARD akan nasarar Adeleke, Kunle Adegoke, babban lauya wanda mamba ne a cikin kungiyar lauyoyin Oyetola ya bayyana cewa lauyoyi 50 ne suka nuna sha’awar shiga shari’ar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Da aka tambaye shi a wani dalili Oyetola zai kalubalanci nasarar Adeleke, Adegoke ya ce suna ci gaba da binciken sakamakon zaben ne dan gina shaida.
A halin da ake ciki kuma, wani jigo a jam’iyyar PDP, Diran Odeyemi, ya shaida wa Vanguard cewa,
“Duk wani dan siyasa da ya ya shirya kalubantar zababben gwamnan jihar Osun, Adeleke, ya sani zai yiwa lauyoyi kyautar kudine kawai.
“Mafi akasarin yan siyasar Najeriya ba sa yarda da shan kaye a zabe har sai sun kai ga kotun koli. Sabida haka hankalinmu a kwance yake.
Zaben Jihar Osun: 'Mun rungumi ƙaddara' - Adamu Abdullahi
A wani labari kuma, Shugaban Jam’iyyar APC na kasa, Senata Abdullahi Adamu, ya ce faduwar APC a zaben gwamnan jihar Osun jarrrabawa ce daga Allah. Rahoton BBC
Abdullahi Adamu ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da yayi da BBC HAUSA, inda yace :
“Ya zama dole mambobin jam’iyyar APC su gyara kurakuran su gabanin zaben shugaban kasa na 2023.
Asali: Legit.ng