‘Yan Sanda sun bada shawarar a gurfanar Shugaban APC a kotu bayan bincike

‘Yan Sanda sun bada shawarar a gurfanar Shugaban APC a kotu bayan bincike

  • ‘Yan Sanda sun gudanar da bincike da ya nuna Stephen Leo Ntukekpo yana da kashi a gindinsa
  • Ana zargin Stephen Ntukekpo da amfani da takardun bogi wajen zama shugaban APC a Akwa Ibom
  • Tun a shekarar bara ake ta rigima a kan wanene ainihin Shugaban jam’iyyar APC na reshen jihar

Akwa Ibom - Binciken da ‘yan sanda suka gudanar, ya tabbatar da cewa takardar bogi Stephen Ntukekpo ya yi amfani da ita, wajen zama shugaban APC.

Premium Times ta ce Stephen Ntukekpo ya dare kujerar shugaban jam’iyyar APC na jihar Akwa Ibom ne bayan ya gabatar da wasu takardun kotu na karya.

Jami’an ‘yan sanda sun gudanar da bincike na musamman, kuma a karshe suka bada shawarar a gurfanar da Ntukekpo bisa zargin karya da shiga rigar wani.

Kara karanta wannan

Masu Garkuwa Sun Sace Shugaban Jam'iyyar APC a Hanyarsa Ta Dawowa Da Gonarsa

“Daga hujjojin da mu ke da su a takardun nan, mu na da ra’ayin cewa ta tabbata akwai zargin karya da shiga rigar wani a kan wanda ake zargi, Stephen Leo Ntukekpo.
A dalilin haka mu ke bada shawarar a gurfanar da wanda ake tuhuma a kotu kamar yadda ya dace.”

Binciken DCP Ochogwu Ogbeh

Wannan takarda ta fito ne daga sashen shari’a da gurfanar da masu laifi na bangaren binciken masu laifi watau FCID a hedikwatar rundunar ‘yan sandan Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugabannin APC
APC ta na rantsar da Stephen Leo Ntukekpo Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

DCP Ochogwu Ogbeh ya aika da takardar shawarar ne a ranar 4 ga watan Yuli 2022 zuwa ga mataimakin shugaban ‘yan sanda wanda ke kula da bangaren FCID.

An yi amfani da sunan Sheriff Banki

‘Yan sanda sun yi wannan bincike ne bayan wani jigo a APC, Sheriff Banki ya gabatar da korafi.

A zaben shugabannin APC da Sheriff Banki ya jagoranta a reshen Akwa Ibom, Austin Ekanem ne aka daura a matsayin shugaban jam’iyya, ba Stephen Ntukekpo ba.

Kara karanta wannan

Musulmi da Musulmi: Tinubu ya yi ganawar sirri da fitaccen fasto kan batun Shettima

Amma abin mamaki, sai Banki ya ga sa hannunsa a wata takarda da ke nuna Ntukekpo aka tsaida ya zama shugaba, alhali ba shi ya rattaba hannun ba.

Tribune ta ce Ntukekpo yana da dauri gindin Sanata Godswill Akpabio, wanda tare suke da shugaban APC da sakatarensa, Abdullahi Adamu da Iyiola Omisore.

A kara wa'adin CVR

Ganin shekarar zabe na karasowa a Najeriya, mun samu labari cewa matasan Kungiyar Kirista ta Najeriya, YOWICAN ta na da bukata wajen hukumar INEC.

Kungiyar YOWICAN ta Arewa maso tsakiya ta yi roko ga Hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, ta tsawaita kwanakin rajistan PVC domin mutane su iya zabe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel