Da na fadi warwas inda Buhari bai sanya hannu a dokar zabe ba – Adeleke

Da na fadi warwas inda Buhari bai sanya hannu a dokar zabe ba – Adeleke

  • Sanata Ademola Adeleke, ya ce da ya sha kaye a zabe inda Buhari bai sanya hannu a dokar zabe da aka yi wa kwaskwarima ba
  • Zababben gwamnan jihar Osun ya ce yayi matukar farin ciki da ya ga sakon taya murnar lashe zabe daga shugabankasa Muhammadu Buhari
  • Adeleke ya ce zai kai wa shugabankasa Muhammadu Buhari ziyarar ban girma da zarar ya karbi satifiket din cin zabe

Jihar Osun - Zababben gwamnan jihar Osun, Sanata Ademola Adeleke, ya ce da ya sha kaye a zaben da aka yi ranar Asabar da ta gabata a hannun jam’iyyar, APC, inda shugaba Buhari bai rattaba hannu kan dokar zabe ta 2022 da aka yi wa kwaskwarima ba. Rahoton VANGUARD

Ya ce:

“Na ji dadin nasarar da na samu, domin al’ummar Jihar Osun sun dade suna kwadayin ganin an dawo da kujerar da aka kwace mu su.

Kara karanta wannan

Shugaban APC: Sam ba na raina abokin hamayya, amma dole mu ci zabe a 2023

“Kasancewa na Adeleke na biyu da zai mulki jihar Osun abin mamaki ne. Allah ne kaɗai zai iya yin haka.
adeleke
Da na fadi warwas inda Buhari bai sanya hannu a dokar zabe ba – Adeleke FOTO Legit.NG
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Nayi murmushi lokacin da na ga sakon taya murna daga Shugaba Buhari, na ce wannan hali yana da kyau ga cigabar kasarmu.
“Ina shirin ziyarce shi idan na karbi satifiket. Yawancin lokaci, 'yan adawa ba sa taya juna murna.

A ranar Asabar da ta gabata Hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya INEC ta ayyana Sanata Ademola Adeleke na jam'iyyar PDP a matsayin wanda ya yi nasara a zaben gwamnan Jihar Osun.

Zaben Jihar Osun: 'Mun rungumi ƙaddara' - Adamu Abdullahi

A wani labari Kuma, Shugaban Jam’iyyar APC na kasa, Senata Abdullahi Adamu, ya ce faduwar APC a zaben gwamnan jihar Osun jarrrabawa ce daga Allah. Rahoton BBC Abdullahi Adamu ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da yayi da BBC HAUSA, inda yace:

“Ya zama dole mambobin jam’iyyar APC su gyara kurakuran su gabanin zaben shugaban kasa na 2023. Zaben Osun ya nuna mana cewa akwai aiki a gabanmu, dole ne mu gyara abubuwan da mu ke yi ba daidai ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Tofa avatar

Ibrahim Tofa