Yadda rikicin cikin gida ya raba kan APC, ya sa PDP ta karbe mulki a jihar Osun
- Fadan da ake yi tsakanin ‘Ya ‘yan APC ya taimakawa Jam’iyyar PDP a zaben Gwamnan Osun
- Bincike ya nuna Ademola Adekele ya ci riba da rikicin Adegboyega Oyetola da Rauf Aregbesola
- ‘Dan takarar jam’iyyar PDP, Sanata Ademola Adekele ya yi galaba a kan jam’iyyar APC mai mulki
Osun - Rikicin cikin gida da zagon-kasa ya yi wa jam’iyyar APC wajen rasa zaben jihar Osun. Daily Trust ta bayyana haka a wani rahoto da ta fitar.
Gwamna Adegboyega Oyetola wanda yake kan mulki, ya sha kashi a wajen Ademola Adeleke.
Binciken Daily Trust ya nuna jam’iyyar APC ta gagara shawo kan rikicin cikin gidanta kafin zaben, hakan ya yi sanadiyyar da PDP ta lashe zaben.
Har aka shiga zabe, APC mai mulki ba ta iya sasanta bangaren Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola da yaran Gwamna Gboyega Oyetola ba.
Zagon kasa aka yi wa APC?
Ana zargin yaran siyasar Rauf Aregbesola sun yi wa APC makarkashiya, suka fito suka marawa ‘dan takaran jam’iyyar PDP baya wajen doke Oyetola.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Shi kuma Rauf Aregbesola wanda ya yi mulki na tsawon shekaru takwas a jere a Osun, ya tsere zuwa kasar waje a lokacin da ake zaben Gwamnan.
Wani Hadimin Gwamna Oyetola ya bayyana cewa ‘ya ‘yan jam’iyyarsu, sun taimakawa PDP, har aka gagara gane su wanene suke tare da APC.
Sulhu ya gagara
Yunkurin da Bola Tinubu, tsohon Gwamna Bisi Akande da mataimakin shugaban APC, Iyiola Omisore suka yi na sasanta bangarorin, bai iya yin tasiri ba.
Bisi Akande ya yi wa gwamna a jihar ta Osun yayin da Omisore ya taimakawa APC wajen samun nasara a zaben 2018, a lokacin yana jam’iyyar hamayya.
Gwamna bai san siyasa ba?
Jaridar ta ce na zargin Oyetola cewa ba ‘dan siyasa ba ne, bai san yadda zai mu’amalance al’umma ba, duk da bai wasa wajen biyan albashi da hakkokin jama’a.
Ko da ya kada kuri’arsa, Mai girma Oyetola bai tsaya yin magana da magoya bayansa ba, yana gama magana da manema labarai, sai ya kama hanyarsa.
Laifin Buhari ne - Mayaki
Sai aka ji labari wani kusa a APC ya yi bambami, ya ce Ministoci da Gwamnonin APC suka yi wa jam’iyya zagon-kasa, har PDP ta yi nasara a zaben da aka yi.
John Mayaki yana ganin bai kamata Muhammadu Buhari ya bar wasu su na karya jam’iyya ba, ya zargi shugaban kasan da rashin damuwa da harkokin APC
Asali: Legit.ng