2023: Hadimin gwamnan PDP a arewa da dandazon mambobi sun sauya sheƙa zuwa APC

2023: Hadimin gwamnan PDP a arewa da dandazon mambobi sun sauya sheƙa zuwa APC

  • Mai ba gwamna Aminu Waziri Tambuwal na Sokoto shawara ta musamman ya ja masoyansa sun sauya sheka daga PDP zuwa APC
  • Honorabul Ibrahim Gidado, tsohon mamba a majalisar dokokin jihar, ya samu kyakkyawar tarba daga jiga-jigan APC
  • Jihar Sokoto na ɗaya daga cikin jihohin da guguwar sauya sheka ta shiga, mafi akasari daga APC ake komawa PDP

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Sokoto - Babban mashawarci na musamman ga gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto, Honorabul Ibrahim Gidado, ya sauya sheƙa daga jam'iyyar PDP zuwa APC.

Jaridar Leadership ta rahoto cewa tsohon mamba mai wakiltar mazaɓar Sakkwato ta kudu 1 a majalisar dokokin jihar ya bayyana wa duniya maƙasudin ficewa daga PDP.

Gwamna Aminu Tambuwal na Sokoto.
2023: Hadimin gwamnan PDP a arewa da dandazon mambobi sun sauya sheƙa zuwa APC Hoto: Aminu Waziri Tambuwal/facebook
Asali: Facebook

Gidado ya ce shi da dandazon magoya bayansa sun yanke shawarin ficewa daga jam'iyya mai mulkin Sakkwato ne saboda rashin alƙibla da aminci tsakanin jagororin jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Jam'iyyar APC ta lallasa PDP, ta lashe rumfar zaɓen Ministan Buhari a jihar Osun

Haka zalika tsohon ɗan majalisan ya ƙara da cewa sun yanke shiga APC ne, "domin haɗa ƙarfi da ƙarfe da kuma ceto jihar Sokoto daga gwamnatin gwamna Aminu Waziri Tambuwal da ta ba mutane kunya."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamansa ya ce:

"Gwamnati mai ci ta gaza warwas musamman ta ɓangaren cika muradan mutanen da suka zaɓe ta."

Tsohon hadimin gwamnan ya samu kyakkyawar tarba

Gidado ya samu tarba da maraba daga Sanata Aliyu Wamako, jagoran APC na jiha da shugaban jam'iyya reshen jihar, Honorabul Isah Sadiq Achida, tare da shugaban matasan APC, Alhaji Nasir Italy.

Wamakko, wanda ya nuna farin ciki sosai a fuskarsa game da sauya sheƙar Gidado zuwa APC, ya tabbatar masa cewa za'a tafi tare da shi kamar kowa, babu banbanci.

Tsohon hadimin gwamnan ya sauya sheƙa ne tare da rakiyar tsohon kwamishinan ƙasa da gidaje, Nasir Ibrahim Dantsoho, da sauran mambobi, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Jam'iyyar PDP ta yi rashin babban jigo, Sanata mai ci ya fice daga jam'iyyar

A wani labarin kuma kun ji cewa Gwamna Fayemi ya sallami baki ɗaya hadimansa daga bakin aiki

Gwamnan jihar Ekiti mai barin gado, Kayode Fayemi, ya amince da ƙare aikin manyan hadimansa na siyasa daga 31 ga Yuli, 2022.

Yayin da wa'adin mulkinsa ke gab da ƙarewa, gwamnan ya yi haka ne domin miƙa mulki ga sabuwar gwamnati cikin sauki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262