Zaben Osun : An raba Kosai kyauta a gidan ministan harkan cikin gida
- Ana raba kosai kyauta a gidan Minsitan harkan Cikin Gida yayin da ake jira ya iso wurin kada kuri'ar sa
- Ministan Harkokin cikin Gida Rauf Aregbesola, bai je wurin kada kuri'a ba a zaben gwamnan jihar Osun dake gudana
- Jam'iyyu guda goma sha biyar ne za su a fafata a zaben Gwamanan jihar Osun da ake gudana a yau
Jihar Osun - Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, bai isa wurin kada kuri’a ba sa’o’i bayan an fara kada kuri’a a zaben gwamnan jihar Osun. Rahoton PUNCH
Mazauna yankin sun kuma ce har yanzu ba su ga Aregbesola ba, wanda suka ce yakan isa garin sa ne a jajibirin zabe.
Yayin da masu jefa kuri'a ke jeran zuwan Aregbesola, ana raba kosai kyauta a kofar gidansa.
Tsohon gwamnan jihar Osun ya saba kada kuri'a a yankin Ilesa ta Gabas, Ward 8, Polling Unit 1.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cewar hukumar zabe mai zaman kanta, jam’iyyun siyasa 15 ne za a fafata da su a zaben da masu kada kuri’a guda 1,955,657.
INEC ta kuma ce za a gudanar da zaben ne a yankuna 332 na rajista a fadin kananan hukumomi 30 na jihar.
Zaben Osun: Muna sa ido kan abubuwan da ke faruwa – EFCC
A wani labari, Wasu jami’an hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC, sun ce suna lura da yadda abubuwa ke gudana a zaben gwamnan jihar Osun. Rahoton PUNCH
EFCC na cikin jami'an tsaron da aka tura jihar Osun domin sa ido akan yadda zaben ke gudana dan dakile musa saye da siyar da kuri'u.
Asali: Legit.ng