Zaben Osun: Muna sa ido kan abubuwan da ke faruwa – EFCC

Zaben Osun: Muna sa ido kan abubuwan da ke faruwa – EFCC

  • Jami’an hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC suna cikin jami'an dake sa ido a zaben dake gudana a jihar Osun
  • Kwamishinan INEC na jihar Osun ya ce ba aikin su bane hana siya da sayar da kuri'u a lokacin da zabe ke gudana
  • Jami'an hukumar EFCC dake sa ido a zaben jihar Osun dake wakana sun ce ba su kama wani mai laifi ba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Osun - Wasu jami’an hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC, sun ce suna lura da yadda abubuwa ke gudana a zaben gwamnan jihar Osun. Rahoton PUNCH

EFCC na cikin jami'an tsaron da aka tura jihar Osun domin sa ido akan yadda zaben ke gudana dan dakile musa saye da siyar da kuri'u.

Kara karanta wannan

Za mu ba mutanen mu damar daukar bindiga idan yanta'adda suka sake kai mana hari, Gwamnan Ondo

A ranar Alhamis ne Kwamishanan INEC na jihar Osun, Farfesa Abdulganiyu Olayinka Raji, ya bayyana cewa, hana siya da sayar da kuri’u ba aikin su bane, aikin jami’an tsaro ne kamar yadda Legit.NG ta rawaito.

EFCCC
Zaben Osun: Muna sa ido kan abubuwan da ke faruwa – EFCC FOTO PUNCH
Asali: UGC

Kimanin jami’an hukumar shida ne suka isa makarantar firamare ta Saint Peters Ward 1, Unit 1, Iragbiji, jihar Osun, a lokacin da ake cigaba da kada kuri’a.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daya daga cikin jami’an EFCC ya fadawa wakilan jaridar PUNCH, cewa suna wurin ne domin sa ido akan yadda zaben ke gudana. Har yanzu basu kama mai laifi ba.

Haka kuma a Ward 1 Unit 2, Popo, Iragbiji, inda Gwamna Adegboyega Oyetola ya kada kuri’a, an kuma ga jami’an EFCC a wurin

Zaben Osun : Ba Aikinmu Bane mu hana Siyar da Kuri'u, Inji Kwamishinan INEC

A wani labari kuma, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ce ba aikinta ba ne hana sayen kuri’u a lokacin zabe.

Kwamishinan Zabe na INEC a Jihar Osun, Farfesa Abdulganiy Raji, ya bayyana haka a lokacin da yake magana a gidan Talabijin na Channels Television na Daily Sunrise a safiyar ranar Alhamis.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Tofa avatar

Ibrahim Tofa