Da Duminsa: APC Ta Zabi Wanda Zai Maye Gurbin Kashim Shettima a Majalisa
- Jam'iyyar APC mai mulki ta zabi Antoni Janar, Kaka Shehu Lawan a matsayin dan takarar sanata mai wakiltar Borno Central don maye gurbin Kashim Shettima
- Sai dai, abokin takarar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar a yanzu shi ke kan kujerar
- Tsohon gwamna Jihar Taraba wanda kuma shine baturen zabe na APC shine ya tabbatar da hakan a ranar Alhamis
Jam'iyyar APC reshen Jihar Borno ta zabi Antoni Janar na Jihar, Kaka Shehu Lawan a matsayin dan takarar kujerar sanata na Borno Central da a halin yanzu Sanata Kashim Shettima, dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar ke kai.
Baturen zabe na jam'iyyar APC kuma tsohon gwamnan Jihar Taraba, Alhaji Uba Magari yayin sanar da sakamakon zaben da aka yi a sakatariyar jam'iyyar a Maiduguri a ranar Alhamis, 14 ga watan Yuli ya ce tsohon kwamishinan shariar ya samu kuri'u 459 cikin 480 masu kyau, rahoton The Sun.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya bayyana cewa:
"Bayan cika bukatar dokokin zabe, da karfin ikon da shugaban jam'iyyar mu na kasa ya bani, na ayyana Barista Kaka Shehu Lawan, tsohon Antoni Janar, a matsayin zababben dan takarar APC na Borno Central."
Kaka Lawan ya magantu
A jawabinsa na amincewa, Kaka Lawan ya gode wa gwamnan da daligets da suka zabe shi.
Ya bukaci daligets din su tattaro masu zabe su cigaba da rajistan katin PVC.
Lawan ya bada tabbacin yin jagoranci na gari ya kuma bukaci mutane su taya shi da addu'a.
Gwamnan Borno ya yi magana
Gwamna Babagana Zulum na Jihar a jawabinsa, ya bayyana zaben Kaka Lawan a matsayin ikon Allah, yana mai cewa babu wanda zai iya canja kadarar Allah.
Ya ce an zabi tsohon Antoni Janar din ne saboda biyayyarsa, rashin girman kai, sadaukar da kai da aminci.
Asali: Legit.ng