PDP ta shigar da INEC kara dan neman hana Tinubu da Obi tsayawa takara

PDP ta shigar da INEC kara dan neman hana Tinubu da Obi tsayawa takara

  • Jam’iyyar PDP ta bukaci INEC da ta haramtawa jam’iyyar Labour da jam'iyyar APC shiga zaben 2023
  • Jam’iyyar ta bukaci kotun da ta haramtawa ‘yan takarar shugaban kasa na jam’iyyun biyu takara saboda sun sauya sunayen abokan takararsu.
  • PDP ta kuma kafa hujja da cewa kalmar ‘placeholder’ ba ta cikin dokar zaben Najeriya

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Jam’iyyar People’s Democratic Party PDP ta shigar da hukumar zabe na kasa INEC kara a kotu dan neman dakatar jam’iyyar PDP da LP tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023. Rahoton Legit.NG

Jam’iyyar PDP ta nemi a dakatar da Tinubu da Peter Obi daga takara ne saboda sauya mataimakin shugaban kasa da suka yi.

PDP ta kuma kafa hujja da cewa kalmar ‘placeholder’ ba ta cikin dokar zaben Najeriya.

obinna
PDP ta shigar da INEC kara dan neman hana Tinubu da Obi tsayawa takara : FOTO Legit.Ng
Asali: Facebook

PDP ta fadawa Kotu cewa bata yadda Tinubu da Obi su tsaya takarar shugaban kasa ba sai dai in za su cigaba da takarar da wadanda suka gabatar wa hukumar zaben a matsayin mataimakansu na farko.

Kara karanta wannan

PDP ta kai INEC Kotu, ta bukaci a haramtawa Tinubu, Peter Obi neman Shugaban kasa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dan takarar Jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu ya sauya zabin sa na farko, Kabiru Masari da tsohon gwamnan jihar Borno Senata Kashim Shettima.

Shi kuma dan takarar jam’iyyar Labour Party Peter Obi ya sauya zabin sa na farko, Mista Doyin Okupe da Datti Baba Ahmed a matsayin abokin takarar sa.

A ainahin shari'ar da ta shigar PDP na neman kotu ta hana INEC canza sunayen mataimakan 'yan takarar da aka fara gabatar mata tun farko.

2023: Jerin sunayen yan takarar mataimakin shugaban kasa 10 da kwamitin APC ya gabatarwa Tinubu

A wani labari kuma, Kafin bayyana Sanata Kashim Shettima a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa na APC mai mulki, an kafa wani kwamiti don ba wanda ke rike da tutar jam'iyyar, Bola Ahmed Tinubu shawara kan wanda zai tsayar a matsayin abokin takara.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto a ranar Alhamis, 14 ga watan Yuli, kwamitin ya gabatarwa Tinubu da sunayen yan takara 10.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Tofa avatar

Ibrahim Tofa