Saura kwana 2 zaben Osun, Jam’iyya ta sa ‘Dan takarar Gwamna ya janye takara
- PRP ta fasa shiga takarar Gwamna da za ayi a jihar Osun, ta bada dalilin daukar wannan mataki
- Uwar Jam’iyyar ta na zargin wanda aka ba tikitin Gwamna da zama a kasar waje, ya ki yin kamfe
- Za a kafa kwamiti wanda zai binciki Ayowole Adedeji da zargin tattara kudi da sunan yakin zabe
Osun - A lokacin da kusan sa’o’i 48 kadai suka rage a fara gudanar da zaben gwamna a jihar Osun, sai aka ji ‘dan takaran jam’iyyar PRP ya fasa yin takara.
Shugaban majalisar zartarwa na jam’iyyar PRP na kasa, ya yi bayanin abin da ya jawo suka hakura da zabe, Channels TV ta kawo rahoton ranar Alhamis.
Majalisar NEC ta bayyana cewa ‘dan takaran ta a zaben gwamnan, bai shiryawa zaben da kyau ba.
Jam’iyyar ta zargi Ayowole Adedeji da yin zamansa a kasar waje tun da aka ba shi tikitin takaran, bai dawo ba sai ana saura makonni biyu a shiga zabe.
Sakataren jam’iyyar PRP na kasa, Babatunde Alli ya fitar da jawabi na musamman, ya bayyana cewa za a kafa wani kwamiti da zai binciki Ayowole Adedeji.
Daily Trust ta ce ana zargin Adedeji da neman gudumuwa daga jama’a da nufin kamfe, amma ba a san inda ya kai kudin ba, domin bai fita yakin zabe ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Jawabin Sakataren PDP na kasa
“Jam’iyyarmu ta PRP a cikin takaici da matukar damuwa, ta lura da rashin maida hankali wajen kamfe daga ‘dan takararmu a zaben Osun, Ayowole Adedeji.
“Majalisar NEC ta yi la’akari da duka zabin da ake da shi, don haka ta bada umarnin janye takarar PRP daga zaben gwamnan Osun na 16 ga watan Yuli, 2022.
Baya ga haka, ana umartar shugabannin jam’iyya na reshen jihar Osun da su kafa kwamitin mutane biyar domin binciken ‘dan takaran PRP a kan wadannan:
Zama a kasar waje tun da ya samu tikiti, bai dawo ba sai makonni biyu kafin zabe, wanda hakan ya jawo aka gagara yin kamfe da duk wani aikin yakin neman zabe;
Zargin tara kudi a ketare da sunan shugabannin jam’iyya na jiha, jam’iyya ba za tayi wasa da wannan zargin ba. Sai kuma zargin amfani da jam’iyya wajen yin kudi.”
Atiku ya shilla ketare
Saura ‘yan kwanaki a gudanar da zaben Gwamna a jihar Osun, sai aka samu labari rikicin cikin gidan PDP bai lafa ba, dole Atiku Abubakar zai dawo Najeriya.
Bola Tinubu ya dawo ya yi bikin sallah a gida har ya tsaida abokin takara, amma Atiku yana ketare tun bayan da ya samu tikitin takarar shugaban kasa a PDP.
Asali: Legit.ng