Tinubu ya birkita lissafin Gwamnonin Arewa da ya dauko Shettima – Hadimin Buhari

Tinubu ya birkita lissafin Gwamnonin Arewa da ya dauko Shettima – Hadimin Buhari

  • Gwamnonin Arewa maso yamma da na Arewa maso tsakiya sun ci burin samun tikitin jam’iyyar APC
  • Ismail Ahmed ya ce dauko Kashim Shettima da aka yi, ya bata ran mutanen wadannan yankunan
  • Arewa maso yamma sun fi ko ina yawan kuri'u, su kuma 'Yan Arewa maso tsakiya ba ayi da su a siyasa

Abuja - Yankunan Arewa maso yamma da Arewa maso tsakiya sun ji haushin rasa tikitin mataimakin shugaban kasar Najeriya a jam’iyyar APC mai mulki.

Ismael Ahmed ya yi hira da gidan talabijin na Channels TV a ranar Laraba, 13 ga watan Yuli 2022, inda ya yi sharhi a game da takarar shugaban kasa a APC.

Kamar yadda mu ka samu rahoto, Ismael Ahmed ya ce akwai gwamnoni masu-ci da suka sa ran za su samu takarar mataimakin shugaban kasa a zaben 2023.

Kara karanta wannan

Yadda Buhari ya shawo kan Gwamnonin APC a kan zaben Shettima da Tinubu ya yi

A cewar Ahmed, wasu sun dauka za a ba Arewa maso yamma takara saboda kuri’arsu ko kuma mutanen Arewa ta tsakiya da ba su taba shiga fadar Aso Villa.

Wasu ba su ji dadi da zabin Tinubu ba

“Jiya na dawo daga Kano, kuma na san akwai mutane da yawa da suka yi fushi (ba su samu tikitin mataimakin shugaban kasa ba)

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Misali, Arewa maso yamma sun fi kowa kuri’u, kusan fiye da mutane miliyan 20. APC ta na da gwamnoni shida a jihohin nan bakwai.
Bola Tinubu
'Dan takaran APC na 2023 Hoto: Asiwaju Bola Tinubu
Asali: Facebook
Biyar daga cikin gwamnonin su na wa’adinsu na karshe, babu wanda ya yi adawa da ‘dan takaran shugaban kasar a zaben tsaida gwani.
Gwamnan Jihar Jigawa ne kurum ya saye fam, shi ma ya hakura ana daf da za a fara zabe. Wasu sun dauka za ayi la’akari da Arewa ta yamma.

Kara karanta wannan

Don Tinubu ya zabi Musulmi: Jarumin Nollywood Kenneth Okonkwo ya fice daga APC

Arewa maso tsakiya ba su taba samun shugaban kasa ko mataimaki a zamanin farar hula ba, duk da yawansu, ba ayi la’akari da su ba.

Kashim ya cancanta - Ahmed

Tsohon shugaban matasan na jam’iyyar APC ya yi fatali da siyasar addini, ya ce babu wanda ya duba addinin Bola Ahmed Tinubu da za a ba shi takara.

Daily Trust ta rahoto Ahmed yana cewa an dauki Tinubu ne saboda hidimar da ya yi a siyasa, ba addininsa ba, haka zalika zabinsa na Kashim Shettima.

Buhari ya lallabi Gwamnoni

Kun ji labari Gwamnonin APC sun yi zama da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan batun zaben 2023, sun nuna rashin jin dadin abin da ya faru.

Wadannan Gwamnoni sun koka kan yadda Bola Tinubu ya dauko abokin takararsa. Daga baya dai Shugaban kasa ya lallashe su, kuma suka hakura.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng