Takara Musulmi da Musulmi: Babban Jigon APC ya fice daga jam'iyyar
- Batun zaɓo Musulmi a matsayin mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na APC ya bar baya da ƙura a cikin jam'iyyar
- Tsohon shugaban hukumar soji ta ƙasa kuma babban ƙusa a APC, AVM Frank Ajobena, ya sanar da fita daga jam'iyya mai mulki
- Ya ce rashin adalci ne da rashin mutumta kiristocin da ke cikin APC, don haka ba zai iya yaƙin neman zaɓe a matsayin bawa ba
Delta - Wani babban jigon jam'iyyar All Progressive Congress wato APC a jihar Delta, Air Vice Marshal Frank Ajobena (mai ritaya.), ya fice daga jam'iyyar bayan zaɓen mataimakin Tinubu.
Punch ta ruwaito cewa ya yi haka ne domin nuna adawa da matakin Bola Ahmed Tinubu, na haɗa takarar shugaban ƙasa Muslmi da Musulmi.
Tsohon shugaban rundunar sojin saman, wanda babban ƙusa ne a uwar jam'iyya ta ƙasa ya bayyana takarar Musulmi da Musulmi a matsayin, "Babban rashin damuwa da mabiya Addinin Kirista a ƙasar nan."
Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da jigon APC ya fitar, wacce aka raba wa manema labarai kwafinta a Warri ranar Litinin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Legit.ng Hausa ta tattaro muku cewa Tinubu ya zaɓi tsohon gwamnan jihar Borno, Sanata Kashim Shettima a matsayin abokin takararsa a zaɓen shugaban ƙasa 2023.
Meyasa ya fita daga APC?
AVM Ajobena ya ƙara da bayyana cewa rashin adalci ne Tinubu ya yanke wannan matakin, wanda a cewarsa, ya na ganin girman ɗan takarar shugaban ƙasan.
Wani sashin sanarwan ta ce:
"Tinubu ba abokin gabata bane, kuma bana yaƙarsa. Ba hali na bane yin fuska biyu, ba adawa nake yi ba amma duk da ina ƙaunar jam'iyyar APC, ya kamata a yi abinda ya dace."
"Zamu iya kiran wannan matakin (Musulmi da Musulmi) a matsayin wani abu da ke kwatanta girman kai da kuma tsantsar rashin mutunta mu kiristoci da ke cikin APC."
"Wannan cigaban ya nuna karara cewa an ɗauke mu wasu mutane da za'a saye ƙuri'un su cikin sauki, hakan sare wa tsarin Demokaraɗiya guiwa ne. A wane matsayi zan yi aiki a tawagar Kanfe? A matsayin Bawa?"
Bayan haka tsohon jami'in rundunar sojin samana Najeriya ya ce, "Dole mutum ya tsayu kan wani abu ko kuma ya rikito, don haka na fice daga APC."
A wani labarin kuma shugaba Buhari ya ce yana shawan wahala a Mulkin Najeriya, don haka ya ƙagara ya sauka ya koma Daura
Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya ce ba ƙaramar wahala ya ke sha ba domin ya kosa wa'adin mulkinsa ya ƙare ya koma Daura.
Da yake jawabi ga gwamnonin APC da wasu shugabannin siyasa, Buhari ya ce ya gode Allah mutane sun yaba da ƙoƙarinsa.
Asali: Legit.ng