Tsohon Sakataren Gwamnatin Buhari ya fito yana adawa da takarar Musulmi-Musulmi
- Babachir David Lawal ya yi kaca-kaca da Asiwaju Bola Tinubu a kan dauko abokin takara Musulmi
- Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayyan ya ce bai dace a rasa Kirista a tikitin zama shugaban kasa ba
- Lawal bai goyon bayan Kashim Shettima saboda APC za ta yi takarar Musulmi da Musulmi a zaben 2023
Abuja - Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir David Lawal, ya nuna bai goyon bayan Musulmi da Musulmi su tsaya takara a jam’iyyar APC.
Daily Trust ta rahoto Injiniya Babachir David Lawal a ranar Talata, 12 ga watan Yuli 2022, yana cewa bai amince da tikitin Bola Tinubu/Kashim Shettima ba.
Babachir David Lawal wanda an san shi da goyon bayan Bola Tinubu, wannan karo ya shiga sahun masu Allah-wadai da neman takaran ‘dan siyasar a APC.
A wani jawabi da ya fitar a daren yau, tsohon SGF din ya yi kira ga Muhammadu Buhari a matsayinsa na shugaban kasa, ya rusa takarar Kashim Shettima.
“Na yi tunani zan gujewa magana a game da kataborar da babban aboki na, Sanata Bola Ahmed Tinubu ya yi wajen zaben abokin takararsa.
Ni ne mutum na karshe da zan yi wa Tinubu adawar zama shugaban kasa. Dalili kuwa tun a 2011 nake matukar goyon bayan ya gaji Buhari."
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
- Babachir David Lawal
Punch ta rahoto Lawal yana mai cewa bai gamsu a tsaida Musulmi da Musulmi su yi takarar shugaban kasa da mataimaki ba, ya ce hakan yana da hadari.
Tun ba yau ba, Injiniya Lawal ya bayyana cewa ya fadawa Tinubu illar kin daukar Kirista.
Tinubu ya canza yanzu
A cewar Lawal, Tinubu mutumin kirki ne, mai daukar shawara, faram-faram da kuma saukin kai, amma ya ce yanzu wasu ‘yan kanzagi sun fara canza shi.
Mataimakin shugaban kasa: Jiga-jigan APC a arewa maso gabas sun jinjinawa APC da Tinubu kan zabar Shettima
“Za su yi masa karya, su bata sunan wasu, su yi duk abin da za su iya domin neman alfarma, kuma su jawowa na kusa da shi bakin jini, haka aka yi masa.”
- Babachir David Lawal
Babachir Lawal ya soki Shetima da cewa mai kudi ne wanda yake da dogon buri. A dalilin zaben shi, kiristoci za su yi wa APC bore, a cewar ‘dan siyasar.
Abin ya yi yawa - Lawal
Ba zai yiwu ‘dan takara ya fito daga Legas, mataimakinsa daga Borno, shugaban APC na kasa daga Nasarawa, mataimakinsa daga Borno a cewar Lawal ba.
Baya ga haka, shugaban kasa ya fito daga jihar Katsina, ga shugabannin majalisar dattawa na wakilai da mataimakinsa daga jihohin Yobe, Legas da Filato.
Asali: Legit.ng