2023: Cikakkun sunayen dakarun Tinubu da za su kawo masa kujerar shugaban kasa

2023: Cikakkun sunayen dakarun Tinubu da za su kawo masa kujerar shugaban kasa

An san Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da iya dabaru idan aka zo kan maganar siyasar yanki da na kasa.

Don haka, a shirye-shiryensa na ganin ya yi nasara a zaben shugaban kasa na 2023, jagoran jam’iyyar mai mulki na kasa ya tanadi manyan dakarunsa wadanda tuni suka fara yi masa aiki a fadin kasar.

Joe Ibokkwe ya saki jerin sunayen manyan ginshikan Tinubu wadanda za su taimaka wajen lallasa abokan hamayyarsa don ganin cewa ya gaje shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Tinubu
2023: Cikakkun sunayen dakarun Tinubu da za su kawo masa kujerar shugaban kasa Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

A bisa ga jerin sunayen da Igbokwe ya wallafa a Facebook a ranar Talata, 12 ga watan Yuli, gwamnoni, manyan masu fada aji da jiga-jigan jam’iyyar mai mulki na yiwa Tinubu aiki a akalla jihohi 14.

Kara karanta wannan

Gwamnoni 9 sun dira gidan shugaban kasa a Daura, sun sa labule da Buhari

Ga jerin sunayen da jihohinsu a kasa:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

  1. Borno: Ali Modu Sheriff, Kashim Shettima, da Babagana Zulum
  2. Kano: Ganduje, Kwankwaso, Shekarau da Tanko Yakassai
  3. Kaduna: El-Rufai da Uba Sani
  4. Ogun: Abiodun, Osoba, Amosun da Gbega Daniel
  5. Ekiti: Gwamna Kayode Fayemi, Adebayo, Fayose, Oni, Bamidele, da Adeyeye
  6. Osun: Gwamna Oyetola, Baba Akande, Aregbesola da Omisore
  7. Nasarawa: Gwamna Sule da Al-Makura
  8. Edo: Adams Oshiomole da Ize-Iyamu
  9. Bauchi: Adamu Adamu da Yakubu Dogara
  10. Gombe: Inuwa Yahaya da Danjuma Goje
  11. Kwara: AbdulRahman zai yiwa Tinubu aiki
  12. Katsina: Gwamna Aminu Masari, Hadi Sirika, Dikki Radda da Ibrahim Masari
  13. Zamfara: Gwamna Bello Matawalle, Marafa, Yerima, Yari da Shinkafi
  14. Lagos: Gwamna Babajide Sanwo-Olu, Fashola, Gbajabiamila, Baba Olusi, Prophet Odunmbaku.

Ya kara da cewa Tinubu zai yi nasara wanda a cewarsa wannan ne dalilin da yasa Rabiu Musa Kwankwaso na jam’iyyar New Nigerian People Party (NNPP) ya ce ya kamata ya yi a hankali.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Kwankwaso ya gamsu da hadin Tinubu da Shettima

2023: Na sanyawa Tinubu da Shettima albarka, in ji Ali Modu Sheriff

A wani labari, tsohon gwamnan jihar Borno, Ali Modu Sheriff, ya ce ya sanyawa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima albarka.

Sheriff ya bayyana hakan ne a cikin sakon taya murna dauke da sa hannun Cairo Ojougboh, Darakta Janar na kungiyar kamfen din Ali Modu Sheriff.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng