Don Tinubu ya zabi Musulmi: Jarumin Nollywood Kenneth Okonkwo ya fice daga APC
- Fitaccen jarumin fina-finan Nollywood, Kenneth Okonkwo, ya fice daga jam’iyyar APC kan tikitin takarar shugaban kasa na Musulmi da Musulmi
- Kenneth Okonkwo ya ce idan Musulmin Arewa za su iya zaban shugaba Krista daga Kudu mai zai hana su zaban mataimakin Krista daga Arewa
- Idan aka bari takarar musulmi da musulmi ya yiwu, siyasar Kristocin Arewa zai mutu murus har abada
Fitaccen jarumin fina-finan Nollywood, Kenneth Okonkwo, ya fice daga jam’iyyar All Progressives Congress mai mulki kan matakin tikitin takarar shugaban kasa na Musulmi da Musulmi a zaben 2023. Rahoton PUNCH
Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu, a ranar Lahadin da ta gabata, ya bayyana tsohon gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima, a matsayin mataimakinsa, duk da bijirewa takarar yan addini daya da wasu bangarori sukayi.
Jarumin ya sanar da matakin nasa ne a wata wasika da ya raba a shafinsa na Instagram a ranar Litinin.
Ya ce matakin da ya dauka ya zama wajibi ne bayan Tinubu ya bayyana Shettima a matsayin mataimakinsa duk da cewa masu ruwa da tsaki da sauran ‘yan Najeriya sun yi ta cece-ku-ce da ba da shawarar daukan Kiristan daga Arewa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Wani bangare na wasikar ya ce,
“Ku tuna na shiga APC ne saboda alkawari da kundin tsarin mulkin kasa ya ba ta na kawar da duk wani nau’in nuna wariya da rashin adalci a cikin al’umman Nijeriya.
“Wannan akida a yanzu babu shi a jam’iyyar APC, tunda suka nuna wa duniya cewa musulmin Arewa ba zai iya zaben Kristan Arewa a matsayin Mataimakin Shugaban kasa da aka hada takara da Musulmin Kudu ba.
“Idan Musulmi za su iya zabo shugabannin Kiristoci na Kudu, yaudara ce a yi tunanin cewa ba za su iya karbar Mataimakin Shugaba Krista daga Arewa ba. Hakan zai ruguza siyasar Kiristocin Arewa a Najeriya har abada, idan aka bar haka ya yiwu" inji shi.
Harin gidan yarin Kuje: Buhari da shuwagabannin tsaro sun gaza, Ndume
A wani labari kuma, Abuja - Shugaban kwamitin majalisar dattawa akan harkokin soji, Ali Ndume, ya caccaki shugaban kasa Muhammadu Buhari da hafsoshin tsaron kasar kan tabarbarewar tsaro a kasar. Rahoton Premium Times
Mista Ndume, dan majalisar dattawa na jam’iyyar APC mai wakiltar Borno ta Kudu, dangane da mummunan harin da aka kai gidan yarin Kuje a ranar Talata, ya ce shugabancin kasar ya gaza a babban kudirin sa na ga ‘yan kasa.
Asali: Legit.ng