2023: Tinubu ya amince ya zaɓi Musulmi a matsayin mataimaki, Gwamna Ganduje

2023: Tinubu ya amince ya zaɓi Musulmi a matsayin mataimaki, Gwamna Ganduje

  • Gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana wanda Tinubu ya amince zai zaɓa a mataimaki
  • Gwamnan ya ce sun ba ɗan takarar shugaban ƙasan shawarin ya ɗauki Musulmi abokin takara kuma ya amince
  • Ya kuma roki Malaman addinin Musulunci da suka je har fadar gwamnatin Kano su sanya yan takarar APC a kowane mataki a addu'a

Kano - Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya ce jagoran jam'iyyar APC na ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya amince ya ɗauki Musulmi a matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban kasa.

Channels tv ta rahoto cewa gwamnan ya yi wannan furucin ne a wurin wani taro da Malamai 100 a fadar gwamnatin jihar Kano a wani ɓangare na bikin zagayowar Babbar Sallah (Eid El Kabir).

Kara karanta wannan

Kokarin ɗinke ɓarakar APC ya gamu da babban cikas, Jigo kuma shugaban kwamitin sulhu ya fice daga jam'iyyar

Gwamna Ganduje tare da Bola Tinubu.
2023: Tinubu ya amince ya zaɓi Musulmi a matsayin mataimaki, Gwamna Ganduje Hoto: @channelstv
Asali: Twitter

"Mun ba shi shawarin ya zaɓi Musulmi a matsayin abokin takararsa kuma ya amince," a lafazin gwamna Ganduje.

"Takarar Musulmi da Musulmi abu ne a zahirance, ba sabon abu bane a Najeriya."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ganduje ya roki Malamai su yi wa Tinubu addu'a

Gwamna Ganduje ya roki Malamai su taimaka wajen yi wa ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, Bola Tinubu, addu'ar Allah ya ba shi Najeriya a babban zaɓen 2023 da ke tafe.

Haka zalika ya bukaci Malaman su taimaka wa gwamnatinsa da Addu'ar zaman lafiya da cigaba mai ɗorewa har zuwa lokacin da wa'adinta zai ƙare, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Bugu da ƙari, Dakta Ganduje bai gajiya ba ya ƙara da rokon Malaman su sanya mataimakinsa, Yusuf Gawuna, wanda ya lashe zaɓen fidda gwanin APC a cikin Du'a'insu, Allah ya ba shi nasara a zaɓen gwamnan Kano 2023.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Ɗan takarar shugaban kasa na LP ya bayyana mataimakinsa na gaske daga arewa

A wani labarin na daban kuma Rikicin PDP ya tsananta, Kotu ta soke tikitin ɗan takarar gwamna a 2023

Babbar Kotun tarayya mai zama a Abuja ta soke tikitin ɗan takarar da PDP ta tsayar a zaɓen gwamnan jihar Delta 2023.

Alkalin Kotun, Mai shari'a Taiwo Taiwo, ya ce hujjoji masu ƙarfi sun tabbatar da cewa Sheriff Oborevwori, bai cancanta ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel