Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari ya sa labule da gwamnonin APC 9 a Daura

Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari ya sa labule da gwamnonin APC 9 a Daura

  • Gwamnonin cigaba na jam'iyyar APC guda Tara sun kai ziyarar barka da Sallah ga shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari a Daura jihar Katsina
  • Bayan ganawar sirri da Buhari, gwamnonin sun bayyana cewa Tinubu da Shettima za su kara haskaka cigaban APC
  • Gwamnan Imo ya yi ikirarin cewa gwamnoni 22 da APC ke da su, zasu tabbatar da nasarar jam'iyyar a 2023

Daura, Katsina - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, da gwamnonin jam'iyyar APC Tara sun shiga ganawa a mahaifar shugaban, Daura a jihar Katsina, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Gwamnonin sun haɗa da Aminu Bello Masari na jihar Katsina, Abdullahi Ganduje na jihar Kano, Abubakar Bagudu na jihar Kebbi, Abubakar Bello na jihar Neja da Abdullahi Sule na jihar Nasarawa.

Gwamnonin APC a gidan Buhari na Daura.
Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari ya sa labule da gwamnonin APC 9 a Daura Hoto: The Governor Of Niger State/facebook
Asali: Facebook

Sauran gwamnonin sune; Hope Uzodinma na jihar Imo, Kayode Fayemi na jihar Ekiti, Simon Lalong na jihar Filato, da gwamna Malam Nasiru El-Rufa'i na jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Gwamnoni 22 zasu tabbatar jam'iyyar APC ta lashe zaɓen 2023 a jihohin su, Gwamna ya faɗe su

Sun shiga gana wa da shugaban ƙasan ne bisa jagorancin shugaban ƙungiyar gwamnonin cigaba na APC kuma gwamnan Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bayanai sun nuna cewa gwamnonin sun shiga gidan kai da kai na shugaban ƙasan da ke Daura da misalin ƙarfe 1:00 na rana, jim kaɗan bayan haka suka fara taron.

Da yake jawabi bayan gana wa da shugaban kasan, Gwamna Atiku Bagudu,ya ce shugabancin Tinubu-Shettima zai ƙara fito da nasarorin shekaru Bakwai na APC karƙashin gwamnatin Buhari.

A ruwayar Channels tv, Bagudu ya ƙara da cewa ƙungiyarsu ta gwamnonin cigaba da maida hankali tana aiki da ji ba gani son tabbatarda nasara a zaɓen gwamnan jihar Osun da ke tafe.

Yadda APC zata lashe zaɓen shugaban ƙasa a 2023

A nashi ɓangaren, gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo. ya bayyana zaɓem Shettima a msatyin wani mataki da kowa ya amince da shi.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: 'Yan bindiga sun kai hari gidan ɗan takarar gwamna, sun buɗe wuta

Bugu da ƙari. ya ce gwamnonin APC 22 zasu tabbatar jam'iyyar ta lashe zaɓe a jihohin su a babban zaɓen shugaban ƙasa da ke tafe a 2023.

A wani labarin kuma Kokarin ɗinke ɓarakar APC ya gamu da babban cikas, Jigo kuma shugaban kwamitin sulhu ya fice daga jam'iyyar

Shugaban kwamitin sulhu da zaman lafiya na jam'iyyar APC reshen jihar Ribas ya yi murabus daga kasancewa mamban jam'iyya.

Dakta Dawari George, ɗan amutun tsohon ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya sanar da haka ne a wata wasika da ya aike wa shugaban APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262