Yadda Tinubu ya guji gwamnonin Arewa-maso-Yamma, ya dauki Shettima

Yadda Tinubu ya guji gwamnonin Arewa-maso-Yamma, ya dauki Shettima

  • Bola Ahmed Tinubu ya guji daukar gwamnonin Arewa Maso Gabas a matsayin abokin takara duk da matsin lambar da suka yi masa
  • Gwamnonin Arewa Maso Yamma sun fi son Tinubu ya dauki Atiku Baguda ko takwaransa na jihar Kaduna, Nasir El-Rufai a matsayin abokin takara
  • Bola Ahmed Tinubu ya baiwa Gwamnan jihar Borno Zulum tikitin takarar mataimakin shugaban kasa kyauta amma ya ki karba

Najeriya - Cikakken bayani akan yadda dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress, Bola Tinubu, ya kaurace wa zaben gwamnonin Arewa maso Yamma, a matsayin abokin takararsa ya fito. Rahoton PUNCH

Maimakon ya yi kasa a gwiwa akan matsin lamba da gwamnonin suka yi masa, a ranar Lahadin da ta gabata Tinubu ya zabi tsohon gwamnan jihar Borno, Sanata Kashim Shettima.

Kara karanta wannan

Yadda Buhari ya shawo kan Gwamnonin APC a kan zaben Shettima da Tinubu ya yi

An tattaro cewa gwamnonin sun fi son Tinubu ya dauki gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu ko takwaransa na jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, amma tun da farko Tinubu ya ba gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum tikitin takarar.

Shettima
Yadda Tinubu ya guji gwamnonin Arewa-maso-Yamma, ya dauki Shettima : FOTO VANGUARD
Asali: Twitter

An tattaro cewa daya daga cikin dalilan da suka janyo jinkiri a zaben abokin takara shine kin amincewar Zulum ga tayin Tinubu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu majiyoyi sun shaida wa jaridar The PUNCH cewa Tinubu ya bai wa Zulum tikitin takara cikin ruwan sanyi amma ya ki karba.

Wani na hannun damar Tinubu da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce,

“Bisa ga shawarwari da bincike, Zulum shine zabin da ya fi shahara. An sha ba shi tikitin amma ya ki saboda wasu manyan dalilai guda biyu. Na farko shi ne ya yi sha’awar kammala wa’adinsa na Gwamnan Jihar Borno da kuma kammala wasu muhimman ayyuka da ya fara.

Kara karanta wannan

2023: Na sanyawa Tinubu da Shettima albarka, in ji Ali Modu Sheriff

Tsohon ɗan majalisar tarayya da wani babban jigon APC sun yi murabus daga jam'iyyar

Rivers - Wani babban jigo a jam'iyyar APC kuma tsohon mamba a majalisar dokokin tarayya, Elder Chidi Wihioka, ya yi murabus daga jam'iyyar kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Hakan na zuwa ne awanni 24 bayan wani tsohon muƙaddashin daraktan hukumar raya Neja Delta, Dame Ibim Semenitari, ya fice daga jam'iyyar APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Tofa avatar

Ibrahim Tofa