Tinubu ya yanke shawara, ya zabi abokin takararsa – Kwamitin kamfe

Tinubu ya yanke shawara, ya zabi abokin takararsa – Kwamitin kamfe

  • Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressive Congress APC a zaben 2023 ya yanke shawarar daukan Musulmi a matsayin abokin takarar sa
  • Tinubu zai kawai shugaba Buhari ziyara a Daura dan bayyana masa wanda ya dauka a matsayin abokin takarar sa
  • Jawaban da ya fito ya nuna abokin takarar Bola Ahmed Tinubu tsohon gwamna ne da ya fito daga yankin Arewa maso gabashin Najeriya

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Legas - Sanata Bola Ahmed Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC a zaben 2023 ya yanke shawarar akan wanda zai zaba a matsayin abokin takararsa kama yadda jaridar VANGUARD ta rawaito.

Wata majiya mai karfi a kungiyar yakin neman zaben Tinubu da ta bukaci a sakaya sunanta ta tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a ranar Lahadi a Abuja.

Kara karanta wannan

Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya dawo gida daga Faransa ranar Sallah

Majiyar ta ce Tinubu zai bayyana sunan dan takarar a wannan makon.

Tinubu
Tinubu ya zabi abokin takararsa – kungiyar yakin neman zabe : FOTO Premium Times

Mai yiwuwa dan takarar mataimakin shugaban kasa ya kasance tsohon gwamna kuma dan majalisar dattawa daga yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Kuma dan takarar mataimakin musulmi ne kamar yadda Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya fada a ranar Asabar da ta gabata cewa Tinubu ya amince da tikitin takarar musulmi da musulmi,” inji majiyar.

Majiyar ya kara da cewa Tinubu baya tunanin addinin dan abokin takarar da zai dauka, cancanta da iya aikin sa kadai ya dame shi

A ranar Lahadi ne Tinubu zai kai ziyarar Sallah ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari a Daura, Katsina, domin yi masa bayani akan abokin takarar da ya zaba.

Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya dawo gida daga Faransa ranar Sallah

Abuja - Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress, Asiwaju Bola Tinubu, ya dawo Najeriya daga kasar Faransa. Rahoton PUNCH

Tinubu ya bayyana haka a shafin sa na Tuwita, da Instagram a cikin jirgin sama ya rubuta “ hanyar zuwa gida”

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Tofa avatar

Ibrahim Tofa