INEC ta kara tabbatar da Machina da Ekpoudom a matsayin yan takarar da ta sani

INEC ta kara tabbatar da Machina da Ekpoudom a matsayin yan takarar da ta sani

  • Hukumar Zabe na INEC ta yi watsi da zargin da ake mata na cewa ta sauya sunayen wasu yan takara da wasu
  • Shugaban majalissar dattawa da Tsohon ministan Neja Delta su fuskanatr kalubabale akan takarar su
  • Hukumar zabe na INEC ta ce da gangan ake yada labarun karya akan ta dan tozarta mutuncin hukumar

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Yobe - Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta ce ta tsaya kan rahotannin da ta samu daga ofisoshinta na jihohi dangane da zaben fidda gwani na jam’iyya na mazabun Akwa Ibom ta Arewa maso Yamma da Yobe ta Arewa. Rahoton Daily Nigeria

Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan yana fuskantar kalubale akan tikitin Sanatan Yobe ta Arewa, kamar yadda Godswill Akpabio, tsohon ministan harkokin Neja Delta, ke fafatawa da Mista Udom Ekpoudom akan tikitin Sanatan Akwa Ibom ta Arewa maso Yamma.

Kara karanta wannan

Tabdijam: Bidiyon wayar kamfen din Tinubu ta bar 'yan soshiyal midiya baki bude

A wata sanarwa da Festus Okoye, kwamishina a hukumar INEC, ya fitar a ranar Asabar, ya yi watsi da rade-radin da ake cewa hukumar ta sauya sunayen wadanda suka lashe zaben fidda gwani.

Machina
INEC ta kara tabbatar da Machina da Ekpoudom a matsayin yan takarar da ta sani : FOTO Legit.NG
Asali: UGC

Mista Okoye ya ce an jawo hankalin hukumar akan cece-kucen da ake ta yadawa a yanar gizo kan sakamakon wasu zabukan fidda gwani da jam’iyyun siyasa suka gudanar a baya-bayan nan da kuma wasu batutuwan da suka shafi su.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ce ana yada zarge-zargen ne da nufin tozarta mutuncin hukumar musamman zaben yankin Akwa Ibom Arewa maso Yamma da kuma Yobe ta Arewa.

Hukumar INEC ta kara tabbatar da cewa Machina da Ekpoudom sue yan takarar da ta sani a mazabun Yobe ta Arewa da Akwa Ibom ta Arewa maso Yamma.

Gwamnonin APC guda uku sun gana da Nyesome Wike a Fatakwal

Kara karanta wannan

2023: PDP ta yi dabara, ta zabo wanda zai kawo karshen APC a Gombe, inji tsagin dan takara

Jihar Ribas - Gwamnonin jam’iyyar All Progressives Congress guda uku a ranar Juma’a sun isa gidan gwamna Nyesom Wike na jihar Rivers don wata ganawar sirri da za suyi dashi kamar yadda jaridar Premium Times ta rawaito.

Gwamnonin sun hada da Kayode Fayemi na jihar Ekiti, Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas da kuma Rotimi Akeredolu na jihar Ondo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Tofa avatar

Ibrahim Tofa