Dalilin da ya sa na amince na zama abokin takarar Peter Obi – Dati Baba-Ahmed
- Datti Baba Ahmed ya bayyana dalilin da yasa ya amince ya zama mataimakin Peter Obi a zabe mai zuwa
- Ahmed ya ce yana da yakinin Peter Obi ba zai yi albazaranci da dukiyoyin Najeriya ba ganin yadda ya mulki jihar Anambara a lokacin da yayi gwamna
- Jam'iyyar Labour Party ta dauki Baba Ahmed a matsayin mataimakin shugaban kasa dan kasancewar sa musulmi dan Arewa
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Abuja - Da yake jawabi a lokacin da aka kaddamar da shi a Abuja a ranar Juma’a, Baba-Ahmed ya ce ya amince da zama abokin takarar Obi ne saboda ya gamsu da nagarta, jajircewa da kwarewanshi, zai iya kawo ma Najeriya gyaran da take bukata kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.
Ya kara da cewa yana da yakinin Obi ba zai yi albazaranci da dukiyar kasar ba, ganin yadda yayi kafa-kafa da dukiyar jihar Anambara a lokacin da yayi gwamna.
Darakta Janar na yakin neman zaben Peter Obi, Dakta Doyin Okupe, wanda ya kasance dan rikon kwarya na takarar mataimakin shugaban kasa, ya yi murabus a ranar Alhamis.
Saukan Doyin Okupe daga mukamin mataimakin shugabankasa ya ba jam’iyyar damar daukan maitaimaki musilmi daga yankin Arewa dan kwatanta adalci.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Jam’iyyar LP ta shiga tattaunawar hadewa da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso’s na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party, (NNPP). Sai dai tattaunawar ta ruguje saboda sun kasa cimma matsaya akan wanda zai yi shugaban kasa da mataimakin shugabankasa.
Takarar Obi ta samu karbuwa sosai a fadin kasar nan musamman a wurin matasa sannan wanda kamfen din sa ya koma #Obidient Movement mai taken: # TakeBackNaija.
Dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar LP, Sanata Yusuf Datti Baba-Ahmed mai shekaru 46 ne mai ilimi, dan kasuwa kuma dan siyasa.
Ya kasance dan Majalisar Wakilai a tsakanin 2003 zuwa 2007, kuma an zabe shi Sanata mai wakiltar Kaduna ta Arewa.
A shekarar 2011, Sanata Baba-Ahmed ya kafa Jami’ar Baze, jami’a mai zaman kanta da ke Abuja, da Jami’ar Baba-Ahmed, Kano (mai jiran lasisi).
Tsohon Firai ministan Japan Da Aka Harba A Gangamin Yakin Neman Zabe Ya Mutu
A wani labari, Japan - Tsohon Firayim Ministan Japan, Shinzo Abe, wanda aka harbe shi a lokacin da yake jawabi gabanin zaben majalisar dattawa da za a yi a ranar Lahadi, ya mutu. Rahoton Daily Trust
An harbi Abe a kirji da wuya a yammacin ranar Alhamis a birnin Nara.
Asali: Legit.ng