Rikicin PDP: Ayu Ya Dawo Kasar Yayin Da ake yunkurin tsige shi
- Shugaban jam'iyyar PDP na kasa Dr Iyorchia Ayu, ya dawo kasar bayan shafe makwanni biyu yana hutu
- Magoya bayan Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ke matsin lamba sai Ayu yayi murabus daga kujerar shugabancin jam'iyyar PDP
- Wani jigo a jam'iyyar PDP ya bayyana cewa baya yiwuwa dan takarar shugabankasa da shugaban jam'iyya su fito daga yanki daya
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Abuja - Shugaban jam'iyyar PDP na kasa Dr Iyorchia Ayu, ya dawo kasar bayan shafe makwanni biyu yana hutu kamar yadda jaridar Daily Trsut ta rawaito.
Makircin tsige shi ya yi kauri ne lokacin da baya kasar yayin da wasu jiga-jigan jam’iyyar suka bukaci ko dai ya sauka ko a nuna masa kofar fita.
Rikicin ya fara na tun daga lokacin da aka tsayar da Gwamna jihar Delta a matsayin mataimakin shgaban kasa na jam’iyyar PDP.
Kwanaki bayan Atiku ya bayyana zabin Okowa, ya tafi Dubai duk da cewa Ayu ma ya tafi hutu a kasar waje ya wanda rashin su a kasar yasa barakar ta karu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Rikicin ya barke ne bayan fitowar Gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam'iyyar PDP.
Wasu a jam’iyyar tare da mambobin BOT, sun fadawa jaridar Daily Trust cewa rashin su a kasar ya sa aka kasa dinke barakar da jam’iyyar ke fama dashi
Majiyoyi da dama sun cewa magoya bayan Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ke kira ga Ayu ya yi murabus, wanda suna ganin tsohon shugaban majalisar dattawan ya goyi bayan Atiku.
Kwamitin da aka kafa don zabar abokin takarar Atiku sun ba da shawarar daukar Wike.
A safiyar Juma’a, Simon Imobo-Tswam Ayu hadimin kan harkokin sadarwa da dabaru, ya tabbatar da cewa shugaban PDP ya dawo kasar.
Wani jigo a jam’iyyar ya bayyana cewa a shekarar da ta gabata an samu fahimtar juna kafin babban taron jam’iyyar na kasa, cewa bai kamata tikitin takarar shugaban kasa da na shugaban jam’iyyar ya fito daga yanki daya ba.
Matan tsohon fitaccen mawaki Eedris Abdulkareem zata bashi kodanta
A wani labari kuma, Jihar Legas - Wani na kusa da iyalan mawaki Eedris Abdulkareem ya shaida wa jaridar TheCable Lifestyle cewa matar mawakin ta dauki nauyin ba wa mijinta kodarta bayan an kammala yi masa dukkan nau'ikan gwaje-gwaje.
Abdulkareem, tsohon shahararren mawakin Najeriya, yana fama da ciwon koda.
Asali: Legit.ng