Da walakin: Shugaban Majalisa ya ce akwai hadin-baki wajen fasa gidan yarin Kuje
- Sanata Ahmad Ibrahim Lawan ya yi Allah-wadai da harin da aka kai a gidan maza da ke Kuje
- Shugaban majalisar kasar yana ganin an hada-kai da wani na cikin gida ko tsohon hannu
- Da suka kai ziyara domin ganin abin da ya faru, Lawan ya ji haushin ganin babu CCTV a kurkukun
Abuja - Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Ibrahim Lawan ya yi magana a kan harin da wasu ‘yan ta’ddan Boko Haram suka kai a kurkukun Kuje.
Daily Trust ta rahoto Sanata Ahmad Ibrahim Lawan yana cewa harin da aka kai a ranar Talata ya nuna yadda sha’anin tsaro ya tabarbare sosai a Najeriya.
Shugaban majalisar ya bayyana haka ne da ya jagoranci wata tawagar Sanatoci zuwa gidan gyaran halin a unguwar Kuje domin ganin irin ta’adin da aka yi.
Tawagar ta hada da wasu ‘yan kwamitin tsaro da bayanan sirri na majalisar tarayya da shugaban hukumar gidan gyaran hali, Haliru Nababa ya zagaya da su.
Ba za ta yiwu cikin sauki ba
A wajen zagayen ne aka rahoto Lawan yana cewa ba zai yiwu a kai irin wannan hari, ba tare da hadin-kai da sa-hannun wasu da suka san kan kurkukun ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da yake jawabi a ranar Alhamis, Lawan ya kuma yi Allah-wadai da yadda hukumar ta gagara amfani da na’urorin CCTV a Kuje da sauran kurkukun kasar.
Ganin hakan, shugaban majalisar kasar ya umarci shugaban na NCS watau Nababa da ya aikowa majalisa bukatar sayen na’urorin CCTV a kasafin kudin 2023.
“An fada mana cewa ‘yan ta’adda kusan 300 suka kawo hari a gidan mazan. Sun zo a kafa ne, kuma na yi imani ya kamata a ce an gano su.”
“Tun farko ba zai yiwu mutum 300 su zo irin wanan danyen aiki ba tare da sun yi tsari ba, Ya kamata tsarin ya dauki makonni ko fiye da wata.”
“Na yi imani ya kamata jami’an tsaronmu sun iya gano wannan a na’urorinsu a birnin tarayya.”
“Sannan mun zagaye gidan yarin, mun ji takaicin ganin babu CCTV a nan, na’urar daukar hoton da zai adana abubuwan da suka wakana."
“Wannan matsakaicin gidan gyaran hali ne, idan a Abuja, a kurkuku irin wannan babu CCTV, za a iya cewa babu CCTV a wasu kurkuku.”
“Na uku, ganin wadanda aka dauke fitattun ‘yan ta’adda ne, da alamar tambaya. Watakila aikin cikin gida ne, wani mai aiki ko wanda ya yi aiki a nan ne.”
Manyan mutanen da ke Kuje
Ku na da labari cewa duka ‘Yan ta’addan kungiyar Boko Haram da Gwamnatin Tarayya ta ke shari’a da su, sun tsere daga gidan yarin Kuje a Abuja.
A gidan yarin akwai irinsu Hamisu Wadume, Abba Kyari, Abdulrasheed Maina, tsofaffin Gwamnonin da aka yi wa afuwa; Joshua Dariye da Jolly Nyame
Asali: Legit.ng