Da Ɗumi-Ɗumi: Kotu ta soke tikitin ɗan takarar gwamnan PDP a Jihar Delta

Da Ɗumi-Ɗumi: Kotu ta soke tikitin ɗan takarar gwamnan PDP a Jihar Delta

  • Babbar Kotun tarayya mai zama a Abuja ta soke tikitin ɗan takarar da PDP ta tsayar a zaɓen gwamnan jihar Delta 2023
  • Alkalin Kotun, Mai shari'a Taiwo Taiwo, ya ce hujjoji masu ƙarfi sun tabbatar da cewa Sheriff Oborevwori, bai cancanta ba
  • Ya kuma umarci jam'iyyar PDP da hukumar zaɓe ta ƙasa INEC su maye gurbinsa da wanda ya kawo ƙara

Abuja - Mai shari'a Taiwo Taiwo na babbar Kotun tarayya da ke zamanta a Abuja, ya soke ɗan takarar kujerar gwamnan Delta karkashin jam'iyyar PDP, Sheriff Oborevwori a babban zaɓen 2023, Channels tv ta ruwaito.

Da yake yanke hukunci, Mai Shari'a Taiwo ya amince da ikirarin mai ƙara cewa bai kamata a bar Oborevwori ya zama ɗan takarar gwamna na PDP ba saboda zargin ya gabatar da takardun karatu masu cin karo da juna ga INEC.

Kara karanta wannan

Valentine Day: Matashin saurayin da ya kashe budurwarsa ranar masoya zai baƙunci lahira a Jos

Jam'iyyar PDP
Da Ɗumi-Ɗumi: Kotu ta soke tikitin ɗan takarar gwamnan PDP a Jihar Delta Hoto: punchng.com

Bayan haka, Alkalin Kotun ya umarci hukumar zaɓe mai zaman kanta da kuma PDP su maye gurbinsa da wanda ya shigar da ƙara, Olorogun David Edevbie, kasancewar shi ya zo na biyu a zaɓen fidda gwani.

Oborevwori, wanda shi ne kakakin majalisar dokokin jihar Delta, an bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen fidda gwani na ɗan takarar gwamna a PDP, wanda ya gudana ranar 25 ga watan Mayu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda rikicin ya samo asali

Tsohon kwamishinan kuɗi, Olorogun David Edevbie, wanda ya zo na biyu a zaɓen fidda gwanin, ya ɗiga alamar tambaya kan Oborevwori bai cancanci shiga zaɓen ba bisa hujjar tantama a karatunsa da shekarun sa.

Ya roki Kotu ta hana jam'iyyar PDP miƙa sunan Oborevwori a matsayin ɗan takarata na gwamnan jihar Delta a zaɓen 2023.

Bisa Hujjoji masu ƙarfi ne Alkalin Kotun ya yanke cewa kwararan hujjojin da aka baje masa a gaban Kotu, wanda ba tantama a kan su sun nuna ɗan takaran bai cancanta ba saboda shilafa kan takardun karatunsa.

Kara karanta wannan

'Ba zamu duƙa mu roki Wike ba' Saɓani ya kunno kai a PDP kan zuwa a rarrashi gwamnan Ribas

Wane matakin PDP zata ɗauka?

Da yake tsokaci kan hukuncin, shugaban PDP reshen Delta, Kingsley Esiso, ya ce bai karanta ainihin hukuncin Kotun ba bare ya san mataki na gaba da zasu ɗauka.

Jaridar Punch ta rahoto shi yana cewa:

"Ban karanta hukuncin ba, kun san ni Lauya ne masanin doka kuma ina da bukatar nazari a aki kafin na ce komai."

A wani labarin kuma Dirama yayin da wani Mutumi ya fara gudanar da aikin Hajji a Sansanin Alhazai na Kano, Hotonsa ya ja hankali

Wani mutumi ya ja hankalin mutane yayin da ya ayyana cewa tuni ya fara aikin Hajjinsa a sansanin Alhazai na jjihar Kano.

Malam Jibrin Abdu daga garin Gezawa a jihar Kano ya ce zai dawo ya ƙarisa aikinsa tun da akwai dukkanin kayan aiki a wurin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262