Ana wata ga wata: Tsohon shugaban tsagin APC a Ribas ya yi murabus daga jam'iyyar
- Tsohon shugaban tsagin jam'iyyar APC reshen jihar Ribas, Golden Chioma, ya yi murabus daga kasancewar mamba
- Chioma, tsohom ɗan majalisar dokokin jihar ya ce ba zai iya cigaba da zama jam'iyyar da bata san halacci ba, tana watsi da mutane bayan sun mata wahala
- Sai dai bai bayyana jam'iyyar da zai koma ba, amma ya ce a dakace shi na ƴan wasu kwanaki kalilan
Ribas - Makusancin Sanata Magnus Abe kuma tsohon shugaban tsagin jam'iyyar APC a jihar Ribas, Golden Chioma, ya fice daga jam'iyyar, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
Chioma, tsohon mamba a majalisar dokokin jihar Ribas, ya sanar da matakin yin murabus daga kasancewa mamban APC a Patakwal, babban birnin jihar.
Tsohon ɗan majalisar bai bayyana maƙasudin ɗaukar wannan matakin ba, amma ya ce ba zai cigaba da zama a jam'iyyar da, "Mutum ɗaya ke juya akalarta domin amfanuwar mutum ɗaya ba."
'Ba zata saɓu ba' Jam'iyyar APC ta tashi tsaye, ta fara shirin dakile sauya shekar wasu mambobinta zuwa PDP
Ya ce ya tattara kayansa ya bar APC ne saboda gazawar jam'iyyar wajen jawo mutanen da suka mata wahala a jiki ta saka musu, ya jaddada cewa tsarin da jam'iyyar ta ɗakko ya yi muni.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A jawabinsa ya ce:
"Duk mutanen da suka sadaukar da goben su a siyasa domin haɓaka jam'iyyar an watsar da su. Mutanen da ba su san wahalar komai ba su ake jawo wa a jiki ana basu muƙamai."
"Amma waɗan da suka cancanta suka dace da Ofisoshin an ja musu layi saboda dalilan da ba su taka kara sun karya ba. A gani na tsarin saka wa waɗan da suka wahala ya lalace, don haka a yanzu na bar jam'iyyar."
Wace jam'iyya zai koma?
Yayin da aka tambaye shi wace jam'iyyar siyasa ya dosa bayan ficewa daga APC, Chioma ya bayyana cewa, "Zan faɗa muku nan da wasu yan kwanaki."
A wani labarin kuma Gwamnatin tarayya ta fallasa yan ta'addan da take zargi da kai hari Gidan Yarin Kuje da ke Abuja
Gwamnatin tarayya ta zargi ƙungiyar Boko Haram da ɗaukar nauyin harin da aka kai gidan Yarin Kuje da ke Abuja.
Ministan tsaro, Bashir Magashi, ya ce duba da ɓarnar da akayi da dabarun harin, alamu sun nuna manufar da yan ta'addan suka je da ita.
Asali: Legit.ng