Direbobin Keke-Napep sun fadawa Bola Tinubu wanda ya kamata ya tafi da shi a APC
- Kungiyar nan ta Keke Marwa Coalition ta rubuta wasika zuwa ga ‘Dan takaran shugaban kasa a APC
- Matuka Keke Napep sun fadawa Bola Tinubu babu wanda ya kamata ya dauka irin Buba Marwa
- Shugabannin kungiyar sun ce Marwa ya taka rawar gani a NDLEA da wajen taimakawa rayuwarsu
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Abuja - Ganin har yanzu jam’iyyar APC ta rasa wanda za ta ba takarar mataimakin shugaban kasa, masu tuka Keke-Napep sun aikawa Bola Tinubu wasika.
Jaridar Vanguard ta ce kungiyar matukan Keke Napep na kasar nan sun nemi Asiwaju Bola Tinubu ya yi la’akari da Buba Marwa a matsayin abokin takara.
A wasikar da kungiyar 'Keke Marwa Coalition' ta aikawa ‘dan takaran shugaban kasar na zaben 2023, ta ce Janar Buba Marwa (mai ritaya) ya fi kowa dacewa.
Shugaban kasa a 2023: Bana son tsohon hannu ya zama mataimakina, na fi son matashi mai jini a jika, Peter Obi
‘Yan kungiyar ta bakin shugabanninsu na reshen Abuja sun ce shugaban hukumar NDLEA ne zabin talakawan kasar nan a zaben shugaban 2023 da za ayi.
Takardar Akula da Babangida Isa
Shugaban matukan Abuja, Kabiru Usman Akula da Sakatarensa, Babangida Isa suka sa hannu a takardar.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Kabiru Usman Akula da Babangida Isa suka ce kungiyar ta san irin kokarin da Buba Marwa ya yi domin ganin yadda miliyoyin matuka za su samu na abinci.
Abin da ya sa suke goyon bayan Marwa
Takardar ta ce Marwa mai ritaya ne wanda ya yi silar kawo babur mai kafafu uku wanda ake kira Keke Marwa a Legas, a yanzu baburin ya zama ruwan dare.
Independent ta ce an yabawa tsohon gwamnan na Legas a kan namijin kokarin da yake yi wajen yaki da miyagun kwayoyi a hukumar NDLEA ta Najeriya.
2023: Idan Har Ka Ajiye Okowa, Ba Zaka Samu Kuri'an Igbo Ba, Matasan Ohanaeze Sun Gargadi Atiku Da PDP
Wannan yaki da kwayoyi zai taimakawa Bola Tinubu wajen kawo karshen matsalar ta’addanci, ta’adin ‘yan bindiga da duk rashin tsaro idan ya dare mulki.
Duba da wadannan, matukan sun roki Asiwaju Bola Tinubu ya karbi shawararsu, ya zabi tsohon sojan domin ta haka ne zai samu gagarumar nasara a 2023.
A karshe, an nemi Muhammadu Buhari da Gwamnonin APC su goyi bayan tikitin takarar Tinubu-Marwa.
Hadin LP da NNPP
Dazu aka ji labari Doyin Okupe ya zargi Rabiu Kwankwaso da zuwa gidan talabijin yana nuna kabilanci, yana cewa 'Yan Arewa ba za su zabi Peter Obi ba.
Okupe ya ce batun wanda zai iya magance matsalar Najeriya ake yi, don haka babu ruwansu da dadewar Kwankwaso a siyasa ko irin mukaman da ya rike.
Asali: Legit.ng