Peter Obi: A madadin kwararru, 'yan tasha ne ke tafiyar da lamurran kasar nan
- Peter Obi ya daura alhakin halin da ake ciki yanzu a Najeriya kan abubuwan da yan Najeriya suka fi ba fifiko a yayin zabe
- Obi ya bayyana cewa ana daukar yan tasha domin su jagoranci al’amurran kasar nan maimakon a yo hayar kwararru
- Dan takarar shugaban kasar na jam’iyyar Labour Party ya yi kira ga al’ummar Najeriya da su zabi wanda ya cancanta a 2023 don samun mafita
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, ya ce yan tasha ne ke jan ragamar harkokin Najeriya maimakon a samu kwararrun masu lasisi.
Obi ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, 6 ga watan Yuli yayin da ya bayyana a shirin safiya na Arise TV.
Tsohon gwamnan na jihar Anambra ya kara da cewar abubuwan farko da yan Najeriya ke dubawa a yayin zabe shine ya jefa kasar a halin da take ciki a yanzu.
Shugaban kasa a 2023: Bana son tsohon hannu ya zama mataimakina, na fi son matashi mai jini a jika, Peter Obi
Dan takarar shugaban kasar ya ja hankalin yan Najeriya da su tabbata sun zabi dan takarar da ya cancanta a 2023 domin jan ragamar al’amuran kasar, rahoton Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce:
“Yan Najeriya na yawan daukar hayar yan tasha maimakon daukar hayar kwararru don jagorantar kasar.”
Shugaban kasa a 2023: Bana son tsohon hannu ya zama mataimakina, na fi son matashi mai jini a jika, Peter Obi
A gefe guda, mun ji cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, a ranar Laraba, 6 ga watan Yuli, ya magantu a kan wanda yake so ya zama abokin takararsa a babban zaben 2023 mai zuwa.
Obi ya bayyana cewa idan son samu ne, ya fi kaunar matashi mai jini a jika ya zamo masa dan takarar mataimakin shugaban kasa, jaridar Punch ta rahoto.
Ya kara da cewar ya fi son matashi wanda ke da abubuwan gabatarwa da za su tallafawa tikitinsa maimakon sake dauko tsoffin hannu wadanda suke dade a gwamnati.
Asali: Legit.ng