Zaben 2023: Ba zai yiwu na yiwa Peter Obi mataimaki ba, Kwankwaso

Zaben 2023: Ba zai yiwu na yiwa Peter Obi mataimaki ba, Kwankwaso

  • Kwankwaso ya ziyarci jihar Gombe dan kaddamar da offishin NNPP da ganawa da zababbun yan takara a jam'iyyar
  • Rabiu kwankwaso ya ce gogewar sa a siyasa yasa jam'iyyar NNPP ta yi kaurin suna da karbuwa a cikin kankanin lokaci
  • Kwankwaso yace ba zai amince yayi kowa mataimakin shugabankasa ba, saboda hakan na iya janyo rugujewar jam'iyyar NNPP

Jhar Gombe - Rabiu Musa Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar New Nigeria People’s Party, NNPP, a ranar Asabar, ya ce amincewa da zama mataimakin duk wani dan takarar shugaban kasa zai zama sanadiya rugujewar jam’iyyar NNPP. Rahoton jaridar Daily Nigeria

Kwankwaso, ya bayyana haka ne a lokacin da ya ziyarci jihar Gombe domin kaddamar da sabuwar ofishin jam’iyyar NNPP da kuma ganawa da dimbin mabiyansa da zababbun ‘yan takara a jam’iyyar da yake zanta wa da manema labaru.

Kara karanta wannan

Kafin 2023: Tashin hankali a APCn Katsina, dubban mambobi sun fece zuwa PDP

Ya ce dacewar sa a siyasa na tsawon lokacin da dimbin mukaman da ya rike kasar ya taimaka wajen ganin jam’iyyar NNPP ta yi kaurin suna cikin kankanin lokaci.

Daily Nigeria
Zaben 2023 : Kwankwaso ba zai yi kowa mataimaki takara ba Hoto : Daily Nigeria
Asali: UGC

Ya bayyana cewa, irin daukaka da karbuwar da jam’iyyar NNPP ta samu cikin lokacin kadan, duk wani mukami da ya gaza shugabankasa zai janyo rugujewar jam’iyyar NNPP.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kwankwaso ya tabbatar da cewa jam’iyyarsa tana tattaunawa da jam’iyyar Labour Party LP domin yiwuwar hadaka amma babban abin dake kawo cikas, shi ne batun wanda zai zama dan takarar shugaban kasa da wanda zai zama mataimaki kamar yadda jaridar Leadership Hausa ta rawaito.

Bama tilasta wa Almajirai shiga addinin Krista - Cocin ECWA

A wani labari, Cocin Evangelical Winning All (ECWA) ta karyata zargin da ke mata na sauya wa Almajirai adinnin su na musulunci zuwa addinin Krista.

ECWA ta bayyana haka ne yayin da take mayar da martani kan labarin yadda hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta kubutar da wasu matasan musulmai 21 da aka canza musu addini zuwa Kristanci. rahoton jaridar Daily Trsut

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Tofa avatar

Ibrahim Tofa