2023: An Bayyana Sunayen Jiga-Jigan APC 2 Da Tinubu Zai Zabi Mataimakinsa Daga Cikinsu

2023: An Bayyana Sunayen Jiga-Jigan APC 2 Da Tinubu Zai Zabi Mataimakinsa Daga Cikinsu

A yayin da wa'adin da hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta bada na mika sunayen ainihin wadanda za su yi wa yan takarar shugaban kasa mataimaki, dan takarar APC, Bola Tinubu, ya ware sunayen mutum biyu.

The Punch ta rahoto cewa dan takarar shugaban kasar na jam'iyyar APC ya zabi sunayen tsohon gwamnan Jihar Borno da gwamna mai ci na jihar.

Shettima, Tinubu da Zulum.
2023: An Bayyana Sunayen Jiga-Jigan APC 2 Da Za Su Iya Zama Mataimakin Tinubu. Hoto: Vanguard.
Asali: UGC

Majiyoyi daga jam'iyyar sun kuma tabbatar da cewa da farko, sunan gwamna Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai na jerin sunayen saboda rawar da ya taka wurin nasarar Tinubu a matsayin dan takarar APC amma daga bisani masu ruwa da tsaki suka cire sunansa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutum biyun da ake kyautata zaton za su yi wa Tinubu mataimaki suna

Kara karanta wannan

Wike Ya Saki Hoto Da Magana Mai Boyayyen Ma'ana Bayan Jita-Jitar Ganawarsa Da Tinubu a Faransa

1. Sanata Kashim Shettima

Tsohon gwamnan Jihar Borno, Kashim Shettima ya na cikin wadanda ke goyon bayan dan takarar na APC sosai.

Shettima ya nuna biyayyansa kwanaki kadan kafin zaben fidda gwani a wani magana da ya yi inda ya nuna baya goyon bayan Yemi Osinbajo.

Shettima, a martaninsa kan fitowar takara da Osinbajo ya yi ya bayyana mataimakin shugaban kasar a matsayin mutumin 'kirki'. Ya kara da cewa mutanen 'kirki' ba su zama shugabanni na gari amma sun fi dacewa da sayar da gurguru da ice cream.

Bugu da kari, wani majiya daga bangaren Tinubu ya ce Shettima ya dade yana goyon bayan Tinubu.

Kalamansa:

"Shettima, na hannun daman Tinubu, ya kuma sake suna goyon bayansa ga takararsa a yayin da ya kare shi bayan babatun da Tinubu ya yi a Abeokuta (Jihar Ogun) kan cewa wasu na son hana shi takara."

2. Gwamna Babagana Zulum

Duk da cewa ya lashe tikitin takarar gwamna na APC a 2023 a Jihar Borno, majiyoyi na cewa ana kokarin tsayar da Babagana Zulum a matsayin mataimakin Tinubu.

Kara karanta wannan

2023: Gwamnonin APC sun zauna, sun yi shawarwari kan yankin da zai kawo abokin tafiyar Tinubu

Duk da cewa dai Zulum a baya ya ce ya fi son ya cigaba da zama gwamna a yanzu a lokacin da aka masa tayin takarar shugaban kasa ko mataimaki.

Amma, na hannun daman Tinubun wanda ya yi magana kan batun ya tabbatar da cewa dan takarar shugaban kasar na APC zai yanke shawarar karshe kan wanda zai masa mataimaki idan ya dawo daga Faransa.

Ya ce:

"Ana ganin Zulum zai samu karbuwa sosai a arewa duba da kokarinsa musamman duk da ta'addancin Boko Haram."

Ya kara da cewa a halin yanzu mutane biyu ne suka rage a jerin sunayen wanda Tinubu zai zaba su masa mataimaki kuma zai yanke shawara da zarar ya dawo.

Wani majiyar ta ce ana ganin idan an zabi Zulum matsayin mataimakin Tinubu, batun tikitin Musulmi da Musulmi zai rage.

Kalamansa:

"Ina ganin Kiristoci za su yi na'am da shi. Mutum ne mai aiki tukuru kuma za a yi na'am da shi saboda cancanta. Kiristoci za su iya goyon bayansa. Sunansa ya yi fice a ko ina."

Kara karanta wannan

Babbar magana: An yi dirama a majalisa, tsakanin Ahmad Lawan da Okorocha

Zaben 2023: Ba Zan Yi Wa INEC Katsalandan Ba, In Ji Buhari

A bangare guda, Shugaba Muhammadu Buhari ya sake jadada cewa gwamnatinsa za ta tabbatar Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta, INEC, ta yi zabe na adalci kuma cikin zaman lafiya a 2023.

Ya bada tabbacin cewa ba zai yi wa INEC katsalandan ba, yana mai cewa bayan kammala zaben cikin gida na jam'iyyu, yanzu an sa ido ne kan zaben 2023 a Najeriya.

Buhari, a cewar sanarwar da kakakinsa Garba Shehu ya fitar a shafinsa na Twitter, ya yi magana ne a daren ranar Laraba a Lisbon yayin ganawarsa da yan Najeriya da ke zaune a Portugal.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164