Zaben 2023: Gwamnatin Neja ta ba da hutun kwanaki 2 don rajista da karbar PVC
- Gwamnatin jihar Neja ta ba ma'aikata hutun kwanaki biyu domin samun damar rajistar katunan zabe
- Wannan na zuwa ne dab lokacin da wa'adin INEC ta shar'anta ya kusa zuwa karshe a shirin karba da rajistar katin zabe
- Gwamnatin jihar ta kuma bayyana matakai da ake dauka domin ganin jiga-jigan gwamnati sun yi rajista
Neja - Gabanin zaben 2023, Gwamna Abubakar Sani Bello ya ayyana ranar Alhamis 30 ga watan Yuni 2022 da Juma’a 1 ga Yuli 2022 a matsayin ranakun hutu a fadin jihar domin baiwa al’ummar jihar Neja damar mallakar katin zabe na PVC, Channels Tv ta ruwaito.
Gwamnan ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar (SSG), Ahmed Ibrahim Matane ya sanya wa hannu a ranar Alhamis a Minna.
Ya ce hutun, an ba da shi ne don baiwa ma’aikatan gwamnati da masu rike da mukaman gwamnati da kuma ‘yan jihar da suka kai shekaru 18 damar karbar katunansu.
Gwamna Bello ya kuma umarci dukkan kwamishinoni, mashawarta, da manyan jami’ansa da su tafi kananan hukumominsu domin wayar da kan jama’a tare domin su fito rumfunan zabe domin yin rajista da karbar katunan kafin wa'adin INEC, inji BluePrint.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A cewar sanarwar:
“A karshen atisayen ana sa ran kwamishinoni da mashawarta na musamman za su bayar da rahoton sakamakon atisayen a kananan hukumominsu."
Yayin da yake rokon kowa da kowa ya fito kwai da kwarkwata domin karbar katin zabe, gwamnan ya kuma umarci duk wani mai rike da mukamin siyasa da ya mika rahoton sakamakon atisayen a karamar hukumarsa.
Zabe: INEC ta shiga damuwa kan yadda ba a karbar katunan zabe gabanin 2023
A wani labarin, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayyana damuwarta kan yadda ake samun karancin karbar katin zabe na dindindin a jihar Legas.
Kwamishinan zabe na jihar Mista Olusegun Agbaje ne ya bayyana hakan a taron masu ruwa da tsaki na mazabu na shekara-shekara na takwas da aka gudanar ranar Alhamis a Legas.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa majalisar dokokin jihar Legas ce ta shirya taron kan muhimmancin katin zabe na PVC gabanin babban zabe na 2023.
Asali: Legit.ng