Da Ɗumi: Gwamnan arewa na PDP ya canza mataimaki, ya zabi mace ta zama mataimakiyarsa a 2023
- Gwamnan jihar Adamawa na jam'iyyar PDP ya zaɓi shugabar jami'ar ADSU a matsayin wacce zata zama abokiyar takararsa a 2023
- Ahmadu Umaru Fintiri ya ɗauki wannan matakin ne bayan jam'iyyar APC ta tsayar da mace takarar gwamnan jihar a 2023
- Kafin gwamnan ya zaɓo ta, Farfesa Kelatapwa Farauta, ta kasance VC ta jami'ar jihar Adamawa tun 2020
Adamawa - Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na jihar Adamawa ya zaɓi shugabar jami'ar jihar (ADSU), Farfesa Kelatapwa Farauta, a matsayin 'yar takarar mataimaki a zabe gwamna 2023.
Daraktan yaɗa labarai na gwamnan, Solomon Kumangar, shi ne ya tabbatar da cigaban ga jaridar Leadership a wata zantawa ta wayar salula ranar Alhamis.
Kumangar ya ce:
"Ya tabbata cewa mai girma gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ya zaɓi Farfesa Farauta a matsayin yar takarar mataimakiyar gwamna."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Farfesa Farauta ta fito ne daga ƙaramar hukumar Numan a jihar Adamawa, kuma zata maye gurbin Crowther Seth wanda ɗan asalin ƙaramar hukumar Lamurde ne, duk a shiyyar kudancin jihar.
The Nation ta rahoto cewa kafin yanzun, Farfesa Farauta ta kasance shugabar jami'ar jihar Adamawa, (ADSU) tun daga shekarar 2020.
A shekarar 2014, Farfesa Kelatapwa Farauta, ta rike muƙamin shugabar hukumar ba da ilimin bai ɗaya ta jihar Adamawa (ADSUBEB).
Haka zalika ta rike muƙamin kwamishiniyar ilimi daga shekarar 2015-2017, daga nan kuma aka naɗa ta shugabar jami'ar jihar Adamawa da ke garin Mubi.
Bayan haka kuma ta taba aikin koyarwa a a jami'ar Modibbo Adama University (M.A.U) da ke Yola, babban birnin jihar.
Tun a shekarar 1989 ta kammala karatun digirinta na farko a fannin noma da kiyo, B.sc Agricultural Extension, a jami'ar Najeriya dake Nsukka, kuma ta yi aure ta haifi 'ya'ya.
A wani labarin kuma Atiku Abubakar ya magantu kan sabon rikicin da ya ɓarke a jam'iyyar PDP
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ce suna cigaba da ɗaukar matakan rarrashin mambobin da suka fusata.
Tsohon mataimakin shugaban ya ce jam'iyyar zata cigaba da zama tsintsiye maɗaurinki ɗaya don maida hankali kan abinda ke gaba.
Asali: Legit.ng