Masu neman takarar gwamna 3 sun sauya sheka daga APC zuwa PDP a jihar Sokoto

Masu neman takarar gwamna 3 sun sauya sheka daga APC zuwa PDP a jihar Sokoto

  • Jam'iyyar APC ta rasa wasu manyan jiga-jiganta guda uku a jihar Sokoto inda suka koma jam'iyyar PDP
  • Masu sauya shekar sun kasance yan takarar kujerar gwamna a zaben fidda gwanin jam'iyyar da aka gudanar kwanan nan
  • Sun sauya shekar ne sakamakon rashin gamsuwa da sakamakon zaben wanda suka yi zargin an yi magudi

Sokoto - Akalla masu neman takarar kujerar gwamna na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben fidda gwanin da aka yi kwanan nan ne suka sauya sheka zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Sokoto.

Daga cikin wadanda suka sauya sheka daga APC zuwa PDP sun hada da wani dan majalisar wakilai, Hon Abdullahi Balarabe Salame, jaridar Punch ta rahoto.

Salame wanda ke wakiltan mazabar Ilella/Gwadabawaa majalisar dokokin tarayya, ya kasance dan majalisa sau uku, sannan ya yi zango biyu a majalisar dokokin jiha, inda ya rike mukamin kakakin majalisa da kuma mukaddashin gwamnan jihar.

Kara karanta wannan

Jami'in INEC: Kuskure ne Ayyana Machina Matsayin 'Dan Takarar Sanatan Yobe ta Arewa a APC

APC da PDP
Masu neman takarar gwamna 3 sun sauya sheka daga APC zuwa PDP a jihar Sokoto Hoto: tribuneonlineng.com
Asali: Facebook

Hakazalika, tsohon ministan sufuri, Hon Yusuf Suleiman, ya karbi katin shaidar zama dan PDP daga hannun shugaban jam’iyyar a jihar a ranar Asabar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A wata wallafa da ya yi a shafinsa na soshiyal midiya, dan siyasar haifaffen karamar hukumar Isa ya ce yanzu shi dan jam’iyyar ne a jihar sannan ya yi alkawarin aiki don nasarar jam’iyyar.

Wani dan takarar da ya sauya sheka zuwa PDP ya kasance shahararren dan kasuwa mazaunin Sokoto, Alhaji Abdullahi Abubakar Gumbi.

Daya daga cikin hadimansa, wanda ya zanta da manema labarai, ya tabbatar da cewar dan kasuwar wanda ya zama dan siyasa ya sanar da gwamnan jihar, Aminu Waziri Tambuwal, aniyarsa na komawa jam’iyyar kuma an kammala duk wasu shirye-shirye.

Sai dai kuma, majiyar ta ce kwanan nan za a yi gagarumin biki don maraba da masu sauya shekar.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Jerin Sanatocin APC da Suka Sauya Sheka Zuwa PDP da Wasu Jam'iyyu

Ya ce shugabannin siyasa da dama a APC sun nuna shirinsu na komawa PDP da aiki don nasararta a zabe mai zuwa.

Jaridar Punch ta tattaro cewa akalla masu neman kujerar gwamna bakwai karkshin inuwar APC ne suka nuna rashin gamsuwarsu kan yadda dan takarar jam’iyyar, Alhaji Ahmed Aliyu ya bayyana.

Ku tuna cewa yan takara biyu, Abdullahi Balarabe Salame da Alhaji Abubakar Gada,sun janye daga tseren yayin da sauran ukun Honourable Yusuf Suleiman, Abdullahi Abubakar Gumbi da Honourable Faruk Malami Yabo suka bar wajen zaben a yayin da ake tsaka da gudanar da shi.

Dukkaninsu sun ce shugabannin jam’iyyar a jihar sun yi magudi, inda suka yi zargin cewa suna yiwa dan takarar da tsohon gwamna, Aliyu Wamakko aiki, wanda shine ya zama dan takarar jam’iyyar a karshe.

Na damu da yadda Sanatoci ke ficewa daga jam'iyyar APC, Adamu

A baya mun ji cewa shugaban jam'iyyar All Progressive Congress wato APC, Sanata Abdullahi Adamu ya nuna damuwa kan yadda guguwar sauya sheka ta mamaye jam'iyya mai mulki.

Kara karanta wannan

Da dumi-duminsa: Peter Obi ya ziyarci Gwamna Nyesom Wike a Port Harcourt

Daily Trust ta ruwaito cewa Sanatocin APC 7 ne suka sauya sheƙa zuwa wasu jam'iyyun adawa bayan gaza samun tikitin takara a babban zaɓen 2023 da ke tafe.

Da yake jawabi ga manema labarai bayan ganawar sirri da Sanatocin APC, Sanata Adamu ya ce abin takaici ne yadda yan majalisun ke barin jam'iyya mai mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng