Jami'in INEC: Kuskure ne Ayyana Machina Matsayin 'Dan Takarar Sanatan Yobe ta Arewa a APC

Jami'in INEC: Kuskure ne Ayyana Machina Matsayin 'Dan Takarar Sanatan Yobe ta Arewa a APC

  • Wani jami'in INEC cike da kwarin guiwa ya bayyanan cewa kuskure ne kiran sunan Bashir Machimna a matsayin 'dan takarar Sanatan APC na Yobe ta arewa
  • A cewar jami'in, duk da shi ya ci zabn fidda gwani wanda INEC ta lura da shi, jam'iyyar siyasa tana da alhakin bayyana shi matsayin 'dan takararta a zaben gaba
  • Sai dai yace, dokokin zaben da jam'iyya da kuma INEC suka sani ba su bai wa INEC damar karnar Lawan matsayin 'dan takara ba, don haka kotu ce zata warware komai

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Yobe - Wani jami’in hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ya ce ba daidai bane a ambaci Bashir Machina a matsayin dan takarar sanata mai wakiltan Yobe ta arewa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

An dai kaddamar da Machina a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwanin APC da aka gudanar a ranar 28 ga watan Mayu, a Gashua.

Kara karanta wannan

Daga karshe: Ta karewa Ahmad Lawan, INEC ta ce Machina ya lashe zaben fidda gwani

Ahmad Lawan da Bashir Machina
Jami'in INEC: Kuskure ne Ayyana Machina Matsayin 'Dan Takarar Sanatan Yobe ta Arewa a APC. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

Ya samu kuri’u 289 cikin 300 da deliget suka kada a zaben.

Sai dai kuma shugaban APC, Abdullahi Adamu ya mika sunan shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan a matsayin dan takarar jam’iyyar na sanata mai wakiltan yankin.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Machina ya rubuta wasika zuwa ga Adamu inda yake kalubalantar lamarin sannan kuma ya tunkari kotu.

Sai dai kuma, abubuwa sun dauki sabon salo a ranar Juma’a lokacin da ya je ofishin INEC a Damaruru don karbar kwafin sakamakon zaben fidda gwanin na gaskiya, Daily Trust ta ruwaito.

Sakamakon wanda ya nunawa duniya ya yi sanadiyar bayyanar rahotannin cewa INEC ta zabe shi a kan Lawan.

Amma wani babban jami’in INEC ya fada wa Daily Trust cike da karfin gwiwar cewa koda dai takardar ta fito daga hukumar ne, hakan baya nufin ana daukar Machina a matsayin dan takarar APC na Yobe ta arewa.

Kara karanta wannan

2023: Makomar 'Dan Takarar APC, Bola Tinubu a Jihohi 19 na Arewacin Najeriya

Ya ce kawai ya nuna sakamakon zaben fidda gwanin da INEC ta sanyawa ido ne, yana mai cewa jam’iyyar siyasa ce za ta zabi dan takararta.

Da aka nemi ya yi martani kan mika sunan Lawan da APC tayi, sai ya ce hukumar ba za ta amince da hakan ba, kamar yadda yake a dokar zabe ta 2022.

“An hana mu (INEC) wallafa sunan duk wani dan takarar jam’iyya da bai fito ta hanyar zaben fidda gwani da INEC ta sanya ido ba kamar yadda dokar zabe ta tanada.”
“Duk da cewa jam’iyyu suna da code da lambobin sirri don tantance ‘yan takararsu a dukka zabuka, muma (INEC) muna da hurumin tabbatar da ganin cewa wadanda jam’iyyun suka zaba su ne ’yan takarar da suka cika sharuddan da aka gindaya.
“Suma jam’iyyun siyasa sun san wannan tanade-tanaden kuma mun yi tarurruka da dama don bitar dokokin tare. Don haka INEC a matsayinta na hukuma ba za ta shiga ayyukan da za su kawo cikas ga dimokaradiyyar kasar ba.”

Kara karanta wannan

Da dumi-duminsa: Peter Obi ya ziyarci Gwamna Nyesom Wike a Port Harcourt

Kan abun da yake mafita, ya ce, "Abun da ya fi maslaha shine kowane bangare ya tunkari kotun kasar."

Babu Tsuntsu, Babu Tarko: 'Dan Takarar Sanatan Yobe Ta Arewa Ya Ki Janyewa Ahmad Lawan

A wani labari na daban, duka biyu kenan ga shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Ahmad Lawan. 'Dan takarar kujerar sanata mai wakiltar Yobe ta Arewa a karkashin jam'iyyar APC kuma wanda ya ci zaben fidda gwani, Bashir Machina, ya ki janyewa Lawan.

Lawan, wanda ke wakiltar Yobe ta Arewa a majalisar dattawa, ya sha kaye a hannun Bola Ahmed Tinubu a zaben fidda gwani na neman tikitin takarar shugabancin kasa da aka yi a ranar 8 ga watan Yuni.

Da farko an fara bayyana shugaban majalisar dattawan a matsayin 'dan takarar yarjejeniya na jam'iyyar, amma gwamnoni 13 na arewacin Najeriya sun yi watsi da lamarin inda suka ce ya zama dole a mika mulki kudancin kasar nan.

Kara karanta wannan

Sabon hari: Mutum 10 sun mutu, 5 sun hallaka a harin 'yan ta'adda a jihar Benue

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng