Jam'iyyar APC ta shiga ruɗani, bata shirya wa zaben 2023 ba, Mataimakin Atiku ya magantu

Jam'iyyar APC ta shiga ruɗani, bata shirya wa zaben 2023 ba, Mataimakin Atiku ya magantu

  • Abokin takarar Alhaji Atiku Abubakar kuma gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, ya ce alamu sun nuna jam'iyyar APC ta shiga ruɗani
  • Okowa wanda ya bayyana haɗakarsa da Atiku a matsayin mai ƙarfi, ya ce PDP ta shirya lashe zaɓen shugaban ƙasa a 2023
  • Ɗan takarar mataimakin ya ce matakin APC na miƙa mataimakin riko ba dabara bace, hakan ya nuna bata shirya wa zabe ba

Abuja - Gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta ya ce jita-jitar dake yawo cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, Bola Tinubu, ya yi amfani da mataimakin riko a matsayain abokin takararsa alamu ne na ba su shirya wa zaɓen 2023 ba.

Mista Okowa ya yi wannan furucin ne yayin da ya bayyana a shirin 'Siyasa a Yau' na kafar Talabijin Channels TV ranar Talata.

Kara karanta wannan

Dambarwa ta sake ɓallewa a siyasar Kano, Ɗan majalisa ya nemi Kotu ta soke ɗan takarar gwamna na APC

Gwamnan jihar Delta shi ne abokin takarar Atiku Abubakar, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP a babban zaɓen 2023 dake tafe.

Gwamna Okowa na jihar Delta.
Jam'iyyar APC ta shiga ruɗani, bata shirya wa zaben 2023 ba, Mataimakin Atiku ya magantu Hoto: Premiumtimesng.com
Asali: UGC

Premium Times ta rahoto cewa a makon da ya shuɗe, Bola Tinubu, ya miƙa wa hukumar zaɓe mai zaman kanta INEC sunan Kabiru Masari a matsayin mataimakinsa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sai dai jita-jitar da ake yaɗawa ta nuna cewa tsohon gwamnan Legas ɗin ya mika sunan Masari ne a matsayin 'Mai riko' domin cika sharaɗin INEC na 17 ga watan Yuni kuma zai sauya shi nan gaba.

Amma gwamnan Delta kuma ɗan takarar mataimaki na PDP ya ce dabarun APC ba wata basira bace kuma haka ya haifar da ruɗani a cikin jam'iyyar.

Okowa ya ce:

"Muna iya ganin cewa APC ta shiga yanayi mai matuƙar wahala kan batun zaɓo wanda zai zama mataimakin ɗan takararta na shugaban kasa. Muna jin abinda bai kamata muji ɓa cewa sun saka sunan wani a matsayin riko."

Kara karanta wannan

Duk da Tinubu ya lashe zaɓen fidda gwani, Shugaba Buhari ya faɗi ɗan takarar yake so ya gaje shi a APC

"Wannan ba wayau bane, hakan ba zai sa mu yarda cewa sun shirya fuskantar baban zaben ba, akwai ruɗani mai tarin yawa a APC."

Tuni muka wuce wurin a PDP, mun shirya - Okowa

Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na PDP ya ce ba kamar APC ba a PDP tuni suka yanke hukunci kan abokin takara.

Ya ƙara da cewa shi da Alhaji Atiku Abubakar zasu haɗa kwarewar su a shugabanci wajen tafiyar da harkokin Najeriya idan suka ci nasara a 2023.

Da yake ayyana haɗakarsu a matsayin 'mai ƙarfi' Okowa ya bayyana kwarin guiwar cewa PDP ce zata lashe babban zaɓen shugaban ƙasa a 2023.

A wani labarin kuma Rikicin APC a mazaɓar Ahmad Lawan ya bude sabon shafi, wani ɗan takara ya maka Machina a Kotu

Rikici kan tikitin takarar Sanata mai wakiltar Yobe ta arewa ya buɗe sabon babi, yayin da wani ɗan takara, Abubakar Abubakar Jinjiri, ya ƙalubalanci nasarar Bashir Sheriff Machina, a Kotu.

Kara karanta wannan

2023: Wata sabuwa ta kunno kai game da Mataimakin Bola Tinubu, Shugaban APC ya yi magana kan batun

Machina, wanda ya samu kuri'u 289 da zaɓen fidda gwani, yanzu haka yana fafatawa da shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan kan tikitin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262