2023: Gwamnan Bauchi da wani babban Jigon PDP sun sa labule da Wike a Patakwal
- Bayan tafiyar Peter Obi, gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi tare da wani jigon APC sun shiga ganawar sirri da Wike a Patakwal
- Rahoto ya nuna cewa manyan jiga-jigan APC na gudanar da taron cikin sirri, babu tabbacin abinda suke tattauna wa
- Wannan na zuwa ne kwanaki huɗu bayan gwamna Dave Umahi na jihar Ebonyi ya kai wa Wike ziyara
Rivers - Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi da Mataimakin shugaban APC na shiyyar kudu maso kudu, Chief Dan Orbih, yanzu haka sun shiga ganawar sirri da gwamnan Ribas, Nyesom Wike.
Babban mai taimaka wa gwamnan Bauchi ta ɓangaren Midiya, Kelvin Ebiri, shi ya tabbatar da haka ga jaridar Leadership a Patakwal, babban birnin Ribas.
Sai dai babu wani cikakken bayani kan dalilin ganawar jiga-jigan na PDP saboda taron yana gudana ne a sirrance a wani gidan gwamna Wike a Patakwal.
Wannan taron na zuwa ne jim kaɗan bayan tsohon gwamnan Anambra kuma ɗan takarar shugaban kasa a jam'iyyar LP, Peter Obi, ya gana da Wike a gidansa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yan takara na cigaba da zuwa wurin Wike
Mista Obi da gwamna Bala Muhammed, sun ziyarci gwamna Wike ne kwanaki huɗu bayan gwamna Dave Umahi na jihar Ebonyi, ya kai wa Wike ziyara, kamar yadda Channels tv ta rahoto.
Dukkan masu kai ziyarar da kuma wanda ke karban baƙuncin su sun fafata a zaɓem fitar da ɗan takarar shugaban kasa na jam'iyyun APC da kuma PDP.
Gwmana Umahi ya nemi tikitin takara ne a jam'iyyar APC mai mulki yayin da gwamna Wike da takwaransa Bala Muhammed suka nema a jam'iyyar PDP.
Ana tsammanin yawon neman shawari da tattaunawa kan siyasa zai ƙara zafi yayin da ake shirin tunkarar babban zaɓen 2023 bayan jam'iyyun siyasa sun kammala fitar da yan takara.
A wani labarin kuma Shugaban APC na ƙasa ya nuna tsantsar damuwarsa da yadda Sanatoci ke fice wa daga jam'iyya mai mulki
Ya ce a matsayinsa na shugaba ya shiga damuwa ba kaɗan ba, amma shi da abokan aikinsa na NWC sun shirya shawo kan matsalar.
A yan kwanakin nan, Sanatocin APC kusan 7 ne suka tattara kayansu, suka fice daga jam'iyyar zuwa wasu jam'iyyun hamayya.
Asali: Legit.ng