Peter Obi danmu ne amma Atiku za mu yi a kudu maso gabas – Ekweremadu

Peter Obi danmu ne amma Atiku za mu yi a kudu maso gabas – Ekweremadu

  • Tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu ya bayyana dan takarar shugaban kasa da yankin kudu maso gabas za su zaba a 2023
  • Ekweremadu ya ce Peter Obi na Labour Party dansu ne amma ba za su zabe shi ba, inda ya ce dan takarar PDP, Atiku Abubakar za su yi
  • Ya ce Obi ya cancanta amma al'ummar yankin ba za su yi kasadar wastar da kuri'unsu a kansa ba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu, ya bayyana cewa mutanen kudu maso gabas ba za su zabi dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, ba a zaben 2023.

Obi, wanda ya kasance daya daga cikin masu neman takarar shugaban kasa na PDP ya sauya sheka zuwa jam’iyyar Labour Party kafin zaben fidda gwanin jam’iyyar wanda Atiku Abubakar ya lashe.

Kara karanta wannan

Zulum ne ya fi cancanta ya zama abokin takarar Tinubu, in ji kungiyar masu ruwa da tsaki na APC

Duk da kasancewarsa dan yanki daya da Obi, Ekweremadu ya ce kudu maso gabas ba za su iya yin kasadar zabar jam’iyyar Labour Party ba a zaben shugaban kasa na 2023, Daily Trust ta rahoto.

Ekweremadu da Atiku
Peter Obi danmu ne amma Atiku za mu yi a kudu maso gabas – Ekweremadu Hoto: thewhistler.ng
Asali: UGC

Koda dai Ekweremadu ya yi furucin ne jim kadan bayan an sanar da Gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta a matsayin abokin takarar Atiku, yanzu haka bidiyon na nan yana yawo a shafin soshiyal midiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daily Post ta nakalto Ekweremadu yana cewa:

“Ina baku tabbacin cewa kudu maso gabas za ta zabi jam’iyyar People Democratic Party (PDP). Zan iya ba da tabbacin hakan. Babu shakka Peter Obi danmu ne, amma mutum na bukatar zama mai sauya abubuwa. Ya kamata ku tambayi kanku, shin Peter zai iya lashe zaben shugaban kasa? Shin mutanen Gabas za su yarda su watsar da kuri'unsu? Shin za mu iya kasancewa masu bangaranci a al’amuran da suka shafi mutanenmu, ’ya’yanmu, da kuma makomarmu? A'a.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Kwankwaso ya tabbatar da cewar suna kan tattaunawa da Peter Obi don hada gwiwar NNPP da LP

“Ba ma nufin yin abun da za mu yi nadama a gaba. Don haka, yayinda muka yarda cewa Peter ya cancanta, mun yi imanin cewa makomar mutanenmu tana tare da PDP. Don haka muna bukatar mu yanke wannan shawarar a matsayinmu na shugabanni. Zan zauna da mutanenmu in yi musu bayani.
“Tabbass Okowa ya kasance daya daga cikinmu, don haka babu banbanci tsakanin Okowa da Peter a wajen kare ra’ayin kudu. Don haka za mu je sannan mu ba mutanen kudu maso gabas dama.”

Peter Obi ya ziyarci Gwamna Nyesom Wike a Port Harcourt

A wani labarin, mun ji cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party (LP), Mista Peter Obi, ya ziyarci gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike a Port Harcourt a ranar Laraba, 22 ga watan Yuni.

Legit.ng ta tattaro cewa sun shafe tsawon awanni suna saka labule a tsakaninsu a gidan Gwamna Wike da ke Port Harcourt, babban birnin jihar Rivers.

Kara karanta wannan

Dangin gwamna: Muhimman abubuwa 8 da baku sani ba game da abokin takarar Tinubu

Ana dai ta rade-radin cewa Wike na shirin ficewa daga jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP bayan ya fadi a zaben fidda gwanin jam’iyyar sannan kuma aka ki zabarsa a matsayin abokin takarar Atiku Abubakar, wanda zai daga tutar jam’iyyar a zaben shugaban kasa na 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng