Atiku ya tura manya su yi wa Wike danniyar kirji domin gudun a samu cikas a 2023

Atiku ya tura manya su yi wa Wike danniyar kirji domin gudun a samu cikas a 2023

  • Bayan ya ki daukar Nyesom Wike a matsayin abokin takararsa, Atiku Abubakar ya kafa kwamiti
  • Wannan kwamiti zai yi aikin lallashin Gwamna Wike da sauran wadanda suka yi fushi da PDP
  • Wasu daga cikin yaran Wike sun soki wannan lamari, sun ce ba a ganin Mai gidan na su da daraja

Abuja - ‘Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar, ya kafa kwamitin da zai zauna da wasu wadanda aka fusata a jam’iyya.

Rahoton da ya fito daga Punch a ranar Laraba ya bayyana cewa kwamitin da Atiku Abubakar ya kafa zai lallashi Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike.

Alhaji Atiku Abubakar ya dauki wannan mataki domin ganin kan ‘ya ‘yan PDP ya hadu kafin 2023.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Atiku yana ruwa, magoya bayan Wike su na barazana a kan dauko Okowa

A halin yanzu akwai rashin jituwa a jam’iyyar PDP a dalilin kin daukar Gwamna Nyesom Wike a matsayin ‘dan takarar mataimakin shugaban Najeriya.

PDP ta bada shawarar a dauki Nyesom Wike a tikitin 2023, amma ‘Dan takarar jam’iyyar ya yi watsi da maganar, ya tafi da Gwamna Ifeanyi Okowa.

PDP ta na tsoron rasa Ribas

Rahoton yace jagororin jam’iyyar PDP su na ganin wannan mataki da Wazirin Adamawa ya dauka zai iya kawo masa da kuma PDP cikas a zaben badi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Atiku
Atiku Abubakar Hoto: @Atiku.org
Asali: Twitter

Hakan ya biyo bayan sanarwar da aka ji daga wasu magoya bayan Nyesom Wike na sauya-sheka daga PDP tun da su ka ji Dr. Okowa ne abokin takarar Atiku.

Wani babba a PDP ya shaidawa Punch cewa Atiku ya nemi ya zauna da Wike domin ya fada masa ya zabi Okowa a maimakonsa, tun kafin ya sanar da Duniya.

Kara karanta wannan

2023: Jerin abubuwa 5 da su ka jawo Atiku ya ki daukar Wike, ya zabi Okowa a PDP

A karshe hakan bai yiwu ba saboda Gwamnan ya koma Fatakwal a lokacin. Hakan ta sa tsohon mataimakin shugaban kasan ya tura mutane su lallashe shi.

Za a dinke barakar PDP?

A cewar majiyar, mutanen da aka zaba za su yi kokarin shawo kan Gwamna Wike da duk sauran wadanda suke ganin jam’iyyar PDP ba ta yi masu daidai ba.

Amma irinsu Hon. Ogbomna Nwuke wanda yana cikin na-kusa da Wike yana ganin akwai tafka da warwara game da lamarin domin an raina ubangidansa.

Ogbomna Nwuke yake cewa Atiku bai nemi ya zauna da Gwamna Wike ba tun bayan zaben tsaida gwani, don haka ba su bukatar ganin wani kwamiti a yanzu.

Barazanar ‘Obidients’

An rahoto Gwamnan jihar Edo yana cewa mutane sun fara neman mafita dabam domin jam’iyyun PDP da APC sun fita ran su, yanzu duk ba ma ta su ake yi ba.

Da alama Obaseki ya fara sarewa domin ya ce kowane gida aka shiga akwai 'yan ‘Obidients’ watau masoyan Peter Obi da babu ruwansu da APC ko PDP.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Atiku Abubakar ya Zabi Gwamna Okowa a Matsayin Abokin Tafiyarsa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng