Ba dai a 2023 ba: Babangida Aliyu ya sha Peter Obi, ya ce ba zai yi mulki ba sai 2027 ko 2031
- Tsohon gwamnan jihar Neja, Babangida Aliyu, ya bayyana cewa Peter Obi ba zai zama shugaban kasar Najeriya ba a 2023
- Aliyu wanda yace yanzu ya wuri sosai, ya ce Obi zai iya darewa kujerar Buhari amma a 2027 ko 2031
- Ya ce yawancin yan PDP sun so dan takarar shugaban kasar na Labour Party ya sake zama mataimakin Atiku Abubakar a zabe mai zuwa
Tsohon gwamnan jihar Neja, Babangida Aliyu ya bayyana cewa ba lallai ne yan Najeriya sun shirya zabar Peter Obi a matsayin shugaban kasa ba a 2023.
Aliyu wanda ya kasance babban jigo na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya bayyana hakan ne a wata hira da gidal talbijin na Channels.
Ya kuma bayyana cewa mutane da dama a jam’iyyar PDP na ta kamun kafa don Obi ya zama mataimakin shugaban kasar Atiku Abubakar.
Obi shine dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party (LP) a babban zaben shugaban kasa na 2023.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Daily Post ta nakalto Aliyu yana cewa:
“Peter Obi abokina ne na kwarai kuma tsohon mamba na kungiyar tsoffin gwamnoni.
“Mutum ne mai nagarta sosai. Takararsa, ta fuskacin shugaban kasa, ina ganin zai yi suna a yanzu. Amma ba lallai ne ya yi nasara ba sai a 20327, 2031. Amma 2023? Ya yi wuri sosai.
“Koda dai matasa na iya zabarsa, sunansa ba zai sauka a koina ba. Ina shakka idan yan Najeriya sun shirya masa a yanzu a matsayin dan takarar shugaban kasa.
“Da zan so shi a matsayin mataimakin shugaban kasa. Da yawanmu suna na son sa don ya sake zama mataimakin shugaban kasar Atiku.”
Ka ji da matsalolin da ke kanka: Martanin Tinubu ga Atiku kan shaguben abokin takara
A wani labarin, dan takarar shugaban kasa na PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya yi shagube ga abokan hamayyarsa kan jinkirin da suka yi wajen samar da abokan takara na dindindin a tsawon lokacin da hukumar zabe ta kasa mai zaman kansu (INEC) ta diban masu.
A cikin wani jawabi da ya yi, Atiku ya ce ofishin shugaban kasa baya bukatar mutum mai jan kafa wajen zabar abokin takararsa.
Sai dai kuma, sauran yan takarar da ke neman kujerar shugaban kasa a babban zaben 2023 da suka hada da tsohon gwamnan jihar Lagas, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu na APC, tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso na jihar NNPP, tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi na LP da sauransu sun zabi abokan takara na wucin gadi ne.
Asali: Legit.ng