2023: APC na da kwarin guiwa na zabar Masari ya zama mataimakin Tinubu, Sanata Adamu
- Yayin da jita-jita ta fara yawa kan mataimakin Tinubu na riƙo, Shugaban APC, Sanata Adamu, ya ce sun yi komai kan doka
- Abdullahi Adamu ya ce ɗan takarar shugaban ƙasa, Bola Tinubu, da APC ba su taka kowace doka ba yayin miƙa Fom ga INEC
- Bola Ahmed Tinubu ya mika Fom tare da sunan Kabiru Masari a matsayin mataimakin riko kafin a zaɓo na gaske
Abuja - Shugaban APC na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya ce jam'iyya mai mulki ba ta taka kowace doka wajen ayyana sunan Kabiru Masari a matsayin mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa, Bola Tinubu.
Duk da APC ba ta sanar a hukumance cewa Masari ne abokin takarar Bola Ahmed Tinubu ba, amma jigon jam'iyyar, Kabiru Faskari, ya tabbatar da cigaban ga jaridar Channels tv ranar Jumu'a.
Sabuwar matsala ta kunno wa Atiku da Tinubu, Dubbannin mambobin APC, PDP sun canza ɗan takarar da zasu zaɓa a 2023
An yi amanna cewa jam'iyya ta zaɓi Masari ne a matsayin "Mataimakin riko" don kada wa'adin da hukumar zaɓe INEC ta bayar na miƙa mata sunayen yan takarar shugaban ƙasa da mataimakansu ya kare.
Matsala ta taso a APC ana ganin Masari ba zai janye ba
Da yake martani kan tsoron cewa da yuwuwar ɗan takar mataimakin na riko ya ƙi yarda ya janye lokacin da na gaske ya bayyana, Adamu ya ce ko da yaushe APC na tunani mai kyau.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Adamu ya ce:
"Ba mu shiga duniyar jita-jita ba, muna tafiyar da shugabancin mu kan dokar ƙasa. Babu abinda ɗan takarar mu ya yi game da miƙa Fom ɗinsa wanda ya saɓa wa layin dokar ƙasa."
"Duk abinda muka yi zuwa yanzun mun yi shi cikin kula tare da neman shawarin masana doka, kuma muna da tabbaci ba zamu tsaya mu saurari wata jita-jita da ake yaɗa wa ba."
"Muna da natsuwar zuciya kan abin da muka yi. Mummunan zato ake masa kuma mu a wajen mu bamu tunanin haka zata faru."
A wani labarin kuma An gano gawar wata mata cikin yanayi a Abuja, wasu abu biyu na kusa da ita sun ɗaga hankulan mutane
Mutanen garin Kubwa a babbar birni n tarayya Abuja sun wayi gari ranar Litinin cikin tashin han kali.
Bayanai sun nuna cewa mazauna ƙaram in garin sun gan o gawar wata mata a juji tare da gawarwaki biyu a kusa da ita cikin wani yanayi.
Asali: Legit.ng