Abokin takara: An ba Tinubu satar amsa ya tafi da Ministan Buhari idan ya na son cin zabe

Abokin takara: An ba Tinubu satar amsa ya tafi da Ministan Buhari idan ya na son cin zabe

  • North East All Progressive Congress Enlightenment Circle ta na goyon bayan Abubakar Malami
  • Kungiyar ta na ganin Malami SAN ya fi kowa cancanta ya yi takarar mataimakin shugaban kasa
  • Har yanzu Bola Tinubu bai dauki abokin takara a APC ba, don haka kowa yake bada irin shawararsa

Bauchi - Wata kungiya a karkashin jam’iyyar APC mai suna North East All Progressive Congress Enlightenment Circle ta tsoma baki a kan batun takara.

Shugaban North East All Progressive Congress Enlightenment Circle, Alhaji Misbahu Sani Bauchi ya fitar da jawabi na musamman a karshen makon jiya.

Daily Trust ta ce Misbahu Sani Bauchi yana so masu ruwa da tsaki a jam’iyya su ba Abubakar Malami (SAN) takarar mataimakin shugaban kasa a APC.

Kungiyar take cewa babu wanda ya cancanta da wannan kujera illa Ministan shari’a na Najeriya saboda irin rawar da ya taka wajen nasarorin da aka samu.

Kara karanta wannan

Mu na tattaunawa da su Peter Obi - Kwankwaso ya tabbatar da shirin taron dangi a 2023

Kokarin da Malami ya yi a APC

Kamar yadda Misbahu Sani Bauchi yake fada a jawabinsa, da su Abubakar Malami aka kafa jam’iyyar APC tun 2013, kuma su ne suka rike gwamnati.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaban kungiyar yake cewa Ministan yana cikin wadanda suka fitar da alkawuran da APC ta yi tun lokacin jam'iyyun CPC, ACN, ANPP ba su dunkule ba.

Tinubu
Asiwaju Bola Tinubu a Legas Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

Bugu da kari, Malami ya hakura da burinsa na takarar gwamnan jihar Kebbi a 2014, ya janyewa Atiku Bagudu saboda irin biyayyar da yake yi wa jam’iyya.

Taka rawar gani a Gwamnati

Tribune ta rahoto wannan kungiya ta mutanen Arewa maso yamma ta na cewa da aka nada Ministoci a 2015, Malami ne ‘dan autansu a majalisar FEC.

Duk da zamansa mai mafi karancin shekaru, kungiyar ta ce Ministan ya kawo nasarori a ma’aikatasa da suka hada da dawo da kudin da aka sace.

Kara karanta wannan

Abokin takarar Tinubu: Kungiyar APC ta tsayar da gwamnan Neja, Sani Bello

North East All Progressive Congress Enlightenment Circle ta jero wasu nasarorin da Ministan ya samu a ofis, da suka sa ya dace ya zama 'dan takara a APC.

Jaridar ta ce Misbahu Sani Bauchi ya sha alwashin idan Bola Tinubu ya dauki Malami, duk matasan da suke Arewacin Najeriya zasu taya su yin kamfe.

Rubutun Sanusi II a kan 'yan takara

Jawabi ya fito daga Shugaban Ma’aikatan fadar Khalifa Muhammadu Sanusi II, Munir Sunusi Bayero a kan rubutun da ake yadawa da sunan Mai martaba.

Ku na da labari a wannan rubutu, an ga kamar tsohon Gwamnan na CBN ya na goyon-bayan Peter Obi. Bayero ya ce Sanusi II bai da alaka da abin da ake yadawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng