Rikicin takara: Ahmad Lawan ya gundiri mutane bayan shekaru 16 a Sanata Inji Hon. Machina

Rikicin takara: Ahmad Lawan ya gundiri mutane bayan shekaru 16 a Sanata Inji Hon. Machina

  • Bashir Sheriff Machina ya sha alwashin ba zai fasa takarar Sanata a jihar Yobe a zaben 2023 ba
  • Hon. Bashir Machina ya ce duk da mutanen Lawan su na tuntubarsa, ba zai hakura da tikitinsa ba
  • ‘Dan siyasar ya koka a kan Ahmad Lawan, yake cewa ‘Yan Arewacin Yobe sun gaji da shi haka nan

Yobe - Bashir Sheriff Machina wanda ya lashe tikitin APC na Sanatan Arewacin Yobe, ya yi hira da Punch a kan tirka-tirkar da ake yi a jihar Yobe.

Hon. Bashir Sheriff Machina ya yi karin-haske a kan dalilinsa na kin janye takararsa ga Ahmad Lawan wanda shi ne shugaban majalisar dattawa.

A cewar Bashir Sheriff Machina, ba maganar cancanta ake yi ba, mutanen Yobe ta Arewa sun gaji da wakilcin Lawan wanda ya yi Sanata sau hudu.

Kara karanta wannan

Wani Fasto ya fadawa mutane wanda za su zaba tsakanin Tinubu, Atiki da Obi a 2023

A shekara mai zuwa, Lawan zai cika shekara 16 a majalisar dattawa, Machina yake cewa mutanen yankinsa su na neman sabon ‘dan majalisa.

Sheriff ba kanwar lasa ba ne a siyasa

Machina ya bayyana cewa tun 1992 ya zama ‘dan majalisar wakilan tarayya a karkashin jam’iyyar SDP, a lokacin yana ‘dan shekara 26 da haihuwa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Daga 1999 zuwa yanzu, jagoran na APC a yau yake cewa ya taba zama Mai ba Atiku Abubakar shawara a kan harkar siyasa, a lokacin su na mulki.

Bashir Sherrif Machina
Hon. Bashir Sherrif Machina Hoto: muhammed.alhajigarba.90
Asali: Facebook

Haka zalika Machina ya ce ya rike mukamai a jam’iyyun adawa na AC da PDP, ya kuma tabbatar da ana ta faman rokonsa ya yafe tikitinsa na APC.

Tsohon ‘dan majalisar ya ce ya yi aiki da Tinubu a AC, don haka ba zai taba cin amanarsa ba. Sannan ya kuma tabbatar da cewa zai je gaban Alkali.

Kara karanta wannan

Na lura ana neman yi mani taron dangi ne, Bola Tinubu ya fadi dalilin yi wa Buhari gori

Al'umma sun gaji haka - Machina

‘Dan takaran ya yabi Gwamnan Yobe, Mai girma Mai Mala Buni, wanda ya ce bai nuna son kai a kan batun takarar Sanata na yankin Arewacin jihar ba.

An rahoto ‘dan takaran yana cewa ba zai sulhunta da Lawan ba, domin mutanen Arewacin jihar Yobe sun gaji da wakilcin shugaban majalisar dattawan.

"Babu abin da zan iya yi masa illa in fada masa ya hakura da burinsa saboda ra’ayin jama’a. Mutanensa su na neman canji, sun gaji da shi, don haka sai ya je ya huta.”

Akwai kura a APC

Legit.ng Hausa ta tattauna da wani malamin jami'ar jihar Yobe wanda ya fito daga Nguru a jihar Yobe wanda ya tabbatar mana da cewa APC ta na cikin kalubale.

A cewarsa, jam'iyya ta hana wasu shiga takarar kujerar Sanata a yankin, don haka aka ce an yi wa Machina mubaya'a ba tare da sauran 'yan takara sun yarda ba.

Kara karanta wannan

Shugaban kamfe ya kyankyasa inda Abokin takarar Tinubu zai fito daga Jam’iyyar APC

Kamar yadda ya shaida mana, abin da ya faru a zaben gwani ya sa wasu daga cikin wanda suka nemi kujerar suka yi farin jin labarin APC ta bada sunan Lawan.

Tinubu ya yi caca a APC

Ku na da labari Asiwaju Bola Tinubu ya ba INEC sunan Kabir Ibrahim Masari mr, amma da zarar a tsaida ‘dan takarar mataimakin shugaban kasa, za a canza shi.

Abdulazeez Yinka-Oniyangi wanda Shugaban kamfe ne a Arewa maso tsakiya ya ce APC ba ta da matsala saboda ta dauki Tinubu da wani musulmi a zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng