Bukola Saraki na yunkurin hargitsa PDP da shirin sa na barin APC

Bukola Saraki na yunkurin hargitsa PDP da shirin sa na barin APC

- PDP ta shiga dabur-dabur saboda maganar dawowar Saraki

- Ana jin cewa Bukola Saraki na shirin barin Jam’iyyar APC

- Jam’iyyar adawar tace ba za ta bari Saraki ya karbe PDP ba

Mun samu labari cewa kishin-kishin din da ake ji na komawar Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki zuwa Jam’iyyar PDP ya rikita lissafin Jam’iyyar adawar a Jihar Kwara a halin yanzu.

Bukola Saraki na yunkurin hargitsa PDP da shirin sa na barin APC
Watakila Shugaban Majalisa Bukola Saraki zai dawo PDP

Jam’iyyar PDP a Jihar Kwara ta nuna cewa ba za ta amince ta mikawa Shugaban Majalisar ragamar Jam’iyyar idan ya baro APC zuwa PDP ba. Shugaban PDP na Jihar ya gana da Uche Secondus domin ganin cewa Saraki bai karbe Jam’iyyar ba idan ya sauya sheka.

KU KARANTA: Jam'iyyar APC za ta maka Gwamna Fayose a Kotu

PDP ta nuna cewa ba za ta hana Saraki dawowa Jam’iyyar ba amma ba za ta bari ya ja ragamar Jam’iyyar ba. PDP tace duk wanda zai dawo Jam’iyyar, dole yayi biyayya a gida ba kurum a turo sa daga sama ya nemi ya karbe komai ba don kuwa yanzu ba da ba ne.

Akwai alamun cewa Bukola Saraki wanda tsohon Gwamnan Jihar ne na kokarin barin APC. Ko da dai tuni Gwamnan Jihar Abdulfatahi Ahmad ya karyata wannan. Shugaban PDP na Kwara yace ko Saraki sun shigo Jam’iyyar ba za a ba mutanen su mukami ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng