To ka ji: ‘Dan takaran APC ya fadi dalilin janyewa Bola Tinubu takarar shugaban kasa
- Sanata Ibikunle Amosun ya ce ganin goyon bayan da Bola Tinubu ya samu, ya sa shi fasa takara
- Tsohon gwamnan na jihar Ogun yake cewa ya dade da burin zama shugaban kasa, amma ya hakura
- Amosun ya bada labarin yadda Dattawan kasar Yarbawa suka nuna masu dole su hada-kai a 2023
Ekiti - Tsohon gwamnan jihar Ogun, Ibikunle Amosun ya fito ya yi bayanin abin da ya sa ya hakura da neman kujerar shugaban kasa a jam’iyyar APC.
The Cable ta ce Sanata Ibikunle Amosun ya ce ya dauki wannan mataki ne ganin yadda Gwamnonin Arewa suka goyi bayan mulki ya koma kudu.
Amosun ya ce Gwamnonin APC sun nuna Bola Tinubu suke goyon-baya, don haka ya bi sahunsu.
Tsohon gwamnan ya bayyana haka ne da yake yi wa magoya bayansa jawabi a wajen wani gangami da aka shirya a fadar Sarki da ke garin Abeokuta.
Gangami a Abeokuta
An gudanar da gangamin ne domin magoya bayansa sun yi wa Sanatan kyakkyawar tarba a gida.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Da yake jawabi da Ingilishi da kuma Yarbanci, Amosun ya shaidawa mutanensa cewa bai dauki takarar zama shugaban Najeriya abin a mutu ko ayi rai ba.
Kishin kasa ya sha gaban buri
Jaridar ta rahoto Sanatan na Ogun yana cewa burin gashin kansa a neman takara bai wuce 20% ba, yayin da ragowar 80% din na kishin kasa da yankinsa ne.
‘Dan siyasar yake cewa tun shekaru biyu da suka wuce da ya ayyana niyyar takarar shugaban kasa, ya fadawa magoya bayansa zai bi wanda jam’iyya ta ke so.
“Dattawanmu na Yarbawa sun kira mu, suka fada mana idan mu na son shugabanci ya dawo kudu maso yamma. Dole ne mu nemi yadda za mu hada-kai.”
“Ba mu da wata kasa sai Najeriya, kuma na tabbata za ta cigaba. Mu na bukatar mu hada hannu ne kurum, mu marawa Tinubu baya, ya gaji Buhari a 2023.”
Punch ta ke cewa Amosun, Kayode Fayemi, Rt. Hon. Dimeji Bankole su na cikin ‘yan siyasar Yarbawa da suka marawa Bola Tinubu baya a zaben 'dan takara.
Zanga-zanga a Ibadan
Ku na da labari cewa ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga sun addabi yankin Kudu maso yammacin Najeriya a ‘yan kwanakin nan, don haka ne aka fara tashi-tsaye
Matasa da Dattawan kasar Yarbawa sun nuna lokaci ya yi da mutane za su tashi domin su kare kansu daga wadannan hare-hare, don haka aka yi zanga-zanga.
Asali: Legit.ng