Yanzu-Yanzu: Tinubu ya zabi Musulmi a matsayin abokin tafiyarsa a zaben 2023 a APC

Yanzu-Yanzu: Tinubu ya zabi Musulmi a matsayin abokin tafiyarsa a zaben 2023 a APC

  • Yayin da wa'adi ya kusan cika, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana sunan wanda zai yi takara tare dashi a zaben 2023
  • Alhaji Kabir Ibrahim Masari ne aka ayyana a matsayin wanda zai yi tafiya tare da Tinubu a zaben 2023 mai zuwa
  • Majiyoyi sun shaidawa jaridar Daily Trust hakan, lamarin da ke nuni da cewa tikitin Muslmi da Musulmi a APC ya tabbata

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC mai mulki, Asiwaju Bola Tinubu, ya ayyana sunan Alhaji Kabir Ibrahim Masari a matsayin abokin takararsa a zaben shugaban kasa na 2023.

Daily Trust ta rahoto cewa, Tinubu ya bayyana sunansa ne a matsayin wanda zai tsaya takara tare dashi yayin da wa’adin hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) na jam’iyyu su mika sunayen ‘yan takararsu a zaben 2023 ya kare.

Kara karanta wannan

Tarihin ‘Dan takaran Yobe da ya karya lakanin Ahmad Lawan, ya sa shi yin biyu-babu

An zabi abokin tafiyar Tinubu
Yanzu-Yanzu: Tinubu ya ayyana wanda ya zaba a matsayin mataikinsa | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Majiyoyi a sansanin Tinubu da Masari sun tabbatar wa Daily Trust haka ne a yammacin ranar Alhamis.

Dan siyasar da aka fitar din ya fito ne daga kauyen Masari da ke karamar hukumar Kafur a jihar Katsina.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Masari mamba ne a hukumar kula da manufofi da tsare-tsare ta kasa (NIPSS) dake Kuru kusa da Jos, babban birnin jihar Filato, inji rahoton AIT.

Kuma an ce dan uwan Aminu Bello Masari, Gwamnan Katsina na yanzu ne.

Hakazalika, ya taba zama sakataren walwala na jam’iyya mai mulki a zamanin Kwamared Adams Oshiomhole a matsayin shugaban APC na kasa.

Bayan rasuwar ‘Yar’aduwa a 2010, Masari ya koma jam’iyyar maja ta CPC, jam’iyyar da shugaba

Gabanin zaben 2015, CPC ta ruguje tsarinta, inda ta game da wasu jam'iyyu ta zama APC sannan Masari ya koma jam’iyyar mai mulki.

Kara karanta wannan

Dalilin da Yasa na Darzo Okowa A Matsayin Abokin Takarata a 2023, Atiku Abubakar

Akwai rahotannin cewa Tinubu zai maye gurbin Masari kafin zabe saboda kawai ya ayyana sunansa ne domin ya cika wa’adin INEC.

A cewar majiyar:

“Tinubu na ci gaba da shawari kan zabin abokin takararsa. Zai maye gurbin Masari da zarar ya zabi wanda ya dace."

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP ya bayyana Gwamna Ifeanyi Okowa a matsayin abokin takararsa a zaben 2023.

Gwamna ya dura hedkwatar PDP don a tantance shi ya tsaya takara da Atiku

A wani labarin, gwamnan PDP, kuma mai ci a jihar Delta, Ifeanyi Okowa ya dura hedikwatar jam’iyyar PDP da ke Abuja, Channels Tv ta ruwaito.

Zai halarci taron tantance dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar, wanda zai tafi tare da Atiku Abubakar a zabe 2023.

Wasu ‘yan jam’iyyar ne suka tarbe shi cikin ginin hedkwatar da kalaman ‘muna maka murna.'

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.