2023: Majiya Ta Lissfa 'Zunuban' Wike Da Suka Sa Atiku Ya Zabi Okowa
Binciken da Jaridar Vanguard nuna wasu dalilai da suka yi sanadin zaben Gwamna Ifeanyi Okowa na Jihar Delta a matsayin mataimakin Atiku Abubakar a maimakon Gwamna Nyesom Wike wanda da farko ake ganin shine ya fi dace wa.
Wata majiya da ta yi magana da jaridar ta ambaci wasu dalilai da jam'iyyar PDP ta yi la'akari da su yayin tuntubarta hakan kuma yasa aka ajiye Wike.
Rikicin harajin VAT tsakanin Wike da Gwamnatin Tarayya
Majiyar ta ambaci cewa wasu sun tado da batun 'dogewa da Wike ya yi kan batun haraji, musamman abin da ya shafi Jihar Rivers da Gwamnatin Tarayya a kan harajin VAT."
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Halin Wike
Dalilin da aka kawo a nan shine cewa gwamnan na Jihar Rivers ne zai rika kula da tattalin arzikin Najeriya a matsayinsa na mataimakin shugaban kasa idan PDP ta ci zabe a 2023 kuma hakan zai zama abu mai "hatsari sosai a bawa mutum mai hali irin na Wike na kula da shi."
Saukin kan Okowa da diflomasiyya
Akasin Wike, ana yi wa Okowa kallon gwamna mara son tada hayaniya kuma hakan ya sa mutane da dama suna kaunarsa a yankin kudu da wasu yankunan saboda diflomasiyyarsa.
Kasancewar Okowa tsohon sanata a Najeriya
Bugu da kari, Okowa ya taba rike kujerar sanata a baya, ba za mu samu matsala da bangaren masu yin doka ba don haka za a samu alaka mai kyau tsakaninta da bangaren masu zartarwa.
Majiyar ta ce:
"Akwai kuma batun kyautata alaka da majalisa. Dan takarar (Atiku) ya yi bayani kuma yana da gaskiya cewa Okowa, wanda tsohon sanata ne zai fi dacewa ya gina kyakyawar alaka tsakanin bangaren masu yin doka da zartarwa."
Sanatan APC Ya Saka Wa Daliget Da Kujerun Hajji Bayan Sun Dawo Masa Da Kudinsa Don Ba Su Zabe Shi Ba
A wani rahoton, Sanata Smart Adeyemi wanda ya wakilci Kogi West a Majalisar Tarayya, ya bada kujerun Hajji ga mutum biyar cikin daligets din da ya bawa kudi amma ba su zabe shi ba a zaben fidda gwani na APC.
Adeyemi ya rasa damar komawa majalisar ne a yayin da ya samu kuri'u 43 a zaben fidda gwanin, hakan yasa ya zo na uku.
Sunday Karimi, wanda ya samu tikitin jam'iyyar ya samu kuri'u 288, yayin da Muyiwa Aina wanda ya zo na biyu ya samu kuri'u 73.
Asali: Legit.ng